CRI Hausa" />

Zimbabwe Zata Karbi Riga-kafin COVID-19 Daga Kasar Sin

Kasar Zimbabwe tana daga kasashe uku na farko a Afrika da za su karbi alluran riga-kafin COVID-19 daga kasar Sin.
Sauran kasashen Afrikan da zasu karbi riga-kafin a sahun farko su ne Saliyo da Equatorial Guinea.
Jakadan kasar Sin a Zimbabwe, Guo Shaochun, ya bayyana a jiya Talata cewa, baki daya kasar Sin zata samar da riga-kafin kashin farko ga kasashe masu tasowa 14, sauran kasashen su ne Pakistan, Brunei, Nepal, Philippines, Myanmar, Cambodia, Laos, Sri Lanka, Mongolia, Palastinu da Belarus.
Guo ya wallafa sanawar da Wang Wenbin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fitar, inda ya cewa, kasar Sin ta himmatu matuka don samar da riga-kafin cutar COVID-19, domin al’ummun duniya su amfana. Wannan yunkuri zai taimaka wajen bayar da babbar damar samun riga-kafin kuma cikin rangwame ga kasashe masu tasowa.(Ahmad)

Exit mobile version