Ziyarar Asibiti Don Duba Lafiya

Mata a kalla 300,000  ne suke mutuwa a kasashen duniya a ko wacce shekara  a sanadiyar bayan an yi masu tiyata  wadda ake yi masu ta  saboda a samu damar cire jariri, wadda ake kira kuma da suna Caesarean Sections ko CS a takaice, saboda su basu iya haihuwa da kan su.

Wani sabon bincike da aka yi wanda aka wallafa rahotonsa a mujallar aikin likitanci ta Birtaniya, The Lancet, shi ne ya nuna hakan.

Binciken ya ce irin wannan abin  ya fi faruwa ne ga matan da ke kasashe masu tasowa,

Masu binciken sun yi nazarin bayanai ne daga mata masu Juna Biyu Wadanda suka kai har zuwa miliyan 12.

Masu binciken sun gano cewar yawan matan da ke mutuwa a sanadiyyar tiyatar a kasashen Kudu da Hamadar Sahara, a Afirka, ya ninka sau dari na yawan wadanda ke mutuwar a kasashe masu arziki, saboda rashin kayan aiki da kwararrun ma’aikata.

Haka kuma binciken ya nuna cewa kusan kashi 10 cikin 100 na jariran da a ke haifa ta hanyar tiyatar ta CS, ba sa zuwa da rai.

Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas):

Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga dan Adam dadadden abu ne a cikin duniyar tarihi. Don haka, kusan ko wacce al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kariya ko magungunan gargajiya don jinyar cututtukan jiki daga tsirrai da wasu ganyayyaki da suke samu a kauyukansu. Kuma babu mahaluki wanda zai bugi da zai  kirji ya ce ya lalle gaskiya ne ya san a ina ko lokacin da aka fara amfani da ganye (tsiro) a matsayin hanyar jinya da kuma maganin  cututtuka, sai dai kuma dangantaka tsakanin tsirran da lafiya ya wanzu ne tun farkon samuwar dan Adam a doron ƙasa.

Hujja ta kusa da ke bayyana dangantakar ta kut-da-kut tsakanin wadannan an same su ne, cikin wasu kungiyoyin addini da kuma wasu muhimman takardun da suka shafi kayayyakin kimiyya a cikin kabarin Neanderthal man (wanda ake danganta shi da samuwar dan adam) da ke binne tun shekaru dubu sittin (60,000) da suka wuce.

Wani binciken kididdiga wanda kuma ya bayyana cewar wasu daga cikin nau’ukan tsirrai da aka binne da gawar a cikin kabarin duk suna taimakawa wajen magani. Bayannan kuma kicibis din da aka yi wajen binciko sabon tsiro na abinci ko a matse ruwansa wanda yake taimakawa wajen rage radadin da ake fama da shi saboda tsananin zafin ciwo musamman ma zazzabi, na iya samun nasaba ne da kasantuwar wannan ilmin wanda ya wuce, bayannan kuma ya yi amfani a cikin  al’umma, wanda daga karshe ya zama sanadiyar samuwar magani.

Haka kuma a wata kididdigar wani binciken wanda ya nuna cewar yawan mutane da ke zaune cikin karkara kashi 75 zuwa  a duniya, har gobe sun dogara ne da magungunan da wadannan tsirrai ke samarwa a matsayin babbar hanyarsu da suke amfani da ita ta kiwon lafiya. Wannan hanyar kuwa ta maganin gargajiya ta cigaba ne da bunkasa a kasar sin (China) a yau da  kuma kasar Indiya da ma wasu kasashe na duniya wadanda su ka hada har ma da Nijeriya.

Exit mobile version