Ziyarar Gani da Ido: Wuraren Tarihi Masu Ban Mamaki a Jihar Katsina

Daga Muhammad A. Abubakar

GABATARWA

Tarihi abu ne muhimmi da yake da amfani a rayuwar addini, al’ada da kuma zamantakewa.Saboda muhimmancin wannan bangare ya saka a jami’o’idaban-daban a kasarnan akwai Malamai da suke koyar da dalibai darasin nazarin tarihi.Kafin nan ma, tun a da, iyaye da Kakanni musamman a kauyuka sun kasance gaba-gaba wajen tara ‘ya’yansu da jikokinsu suna ba su bayanai dangane da abubuwan dauri domin daukar darasi. Fahimtar tarihi na saka mutum ya fahimci bayansa wanda wannan zai ba shi daman fahimtar yau din shi da kuma shirya ma gobensa. Duk al’ummar da ba ta damu da tarihinta ba, zaka samu al’umma ce wacce take zaune tamkar kara-a-zube, kuma ci gaban al’ummar lamuhalatan zai karanta.Da yake taskace tarihi wani abu ne mai muhimmanci, wanna yasa a duk karshen zangon karatu na farko wato ‘First Semester’, daliban neman tarihi da gina shi (archaeology) na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na gudanar da wani bincike na musamman dangane da abin da ya shafi tarihi a wata jiha da aka yi ittifakin zuwa.

‘Field Archaeology’ a turance ya zama wani zaunannen abu da kowanne dalibi na sashen ya zamar masa farilla ya je, kuma rashin zuwa ko da da wani dalili neyana saka dalibi ya kara shekara guda a karatun digirinsa na farko ne ko na biyu. Daliban da suke zuwa wannan bincike ya hada da dukkan daliban da suke sashen a matakin digiri na farko da na biyu. Dukkan Malaman sashen suma ba su huta ba, domin da su ake tafiyar.Wannan yasa a karshen watan Afrilun 2016 daliban sashen suka gudanar da bincikentarihi a wasu garuruwan jihar Katsina. Daliban wanda suka hada tun daga matakin Aji 2, 3 zuwa ajin karshe wato Aji 4 a matakin digirin farko ke nan, sannan sai dalibai a matakin digiri na biyu, sun gudanar da wannan bincike ne a garuruwan Dabai, Gozaki, Kafur da kuma Yaribori duk a jihar ta Katsina. Cikin ikon Allah, na bi tawagar da suka yada zango ne a garin Dabai dake karamar hukumar Danja a jihar ta Katsina. Kauyen Dabai a halin yanzu yana karkashin karamar hukumar Danja a jihar Katsina. Tafiyar kilimota 9 ce ta gabashin garin Danja ta titin Kafur zuwa Zariya. Ta yi matattara da kauyukan Gozaki ta Gabas, daga yamma kuma da Kauyen Baramo, ta arewanci kuma da Kauyen Kahutu, ta kudanci kuma da Kauyen Tandama. Kauyen Dabai na da yawan Bishiyoyi da ciyawa, a lokacin rani garin na bushewa sakamakon tsananin zafin rana. Suna da yawan bishiyoyin Kuka, Darbejiya, kwakwa, Dabino, Mangoro, Tsamiya. A bangaren gini, mafi yawan gine-ginensu na da ne. Sai dai suna da gine-ginen zamani (a yanzu), sannan yanayin tsarin gine-gine a tsaye yake, kuma kusa da kusa. Ta yadda ba a yi la’akari da hanyoyin wucewar ruwa ba. Sannan har wala yau suna da duwatsu.A yanayi gari kuwa, suna da yanayin damina da rani, sanyi da zafi.

TARIHIN GARIN

Dangane da tarihin garin kuwa, kamar sauran kasashen Hausa, mun samu tarihin wannan garin ne ta hanyar baka, ana kyautata zaton an kafa garin ne a shekarar 1500-1600 AD. Kuma an sakawa garin suna Dabai ne sakamakon gudummawa da sadaukarwar da wani mutum mai suna ‘DABAI’ ya bayar wajen kafa garin. Wanda ya ba da gudummawa a bangaren da ya shafi tattalin arziki da zamantakewa, wannan dalilin yasa al’ummar garin suka maishe da garin da sunansa. Asalin mutumin Bamaguje ne, sannan kuma ba shi da addini, kuma mafi yawan al’ummar Kauyen a wancan lokacin Musulmai ne, amma sun zauna da shi lafiya kuma har suka maida sunan garin da sunan mutumin.Tarihi ya nuna cewa asalin inda shi wannan DABAI ya zauna akwai tazarar kilomita 1 ta titin Kuraku daga inda garin yake a yanzu.A yanzu masarautar Dabai tana karkashin kulawar Iyalan Sarkin Fawa Bagi, Alhaji Dabo Yusuf Gambon Ishali da kuma Dangoggo Bawa.DABAI ya koma garin DAYIwanda yanzu garin ke karamar hukumar Malumfashi a jihar ta Katsina. A karshe tarihi ya nuna cewa; Dabai da dan uwansa tare da iyalansusun zauna a wani Kauye da ake kira Baragungume kafin daga nansu bar garin su koma wani wuri da tarihi bai tantance ba.

TSARIN SIYASAR KAUYEN DABAI

Tarihi bai tantance koyaushe ne masarautar ta yi wani zaunannen tsarin siyasa ba.Sai dai tarihi ya tabbatar da cewa; Kauyen Dabai ya zauna a karkashin tsohuwar masarautar Gozaki, a inda ake kiran sarkin garinda GALADIMAN GOZAKI, sannan ta kasance a karkashin masarautar GOZAKI na kusan shekaru 100. Kafin rushewar masarautar GOZAKI a shekarar 1915, garin Dabai ya zama tamkar Hedikwatan masarautar musamman a shekarar 1868. Bayan tsawon wani lokaci, an fafata yaki a tsakanin Masarautun Katsina da na Gozaki, wanda a karshe sakamakon karfin mulki, siyasa da na tattalin arziki da Masarautar Katsina take da shi, ta yi nasarar yakin akan masarautar ta GOZAKI. Daga nan sarautar DABAI ta koma karkashin masarautar Katsina. Wanda ake kira sunan sarautar sarkin garin Dabai da ‘MAGAJIN DABAI.’Sarautar Dabai a yanzu na karkashin ikon Sarkin Danja ne. Ya zuwa yanzu da kafuwar garin Dabai zuwa yanzu an yi Sarakai daban-daban tun daga tsohuwar masarautar Gozaki wanda ake kiran Sarkin garin Dabai da GALADIMAN GOZAKIzuwa yanzu da ake kiran Sarkin garin da MAGAJIN GARIN DABAI.Sarakan da aka yi sune kamar haka:Sarki Gagari a matsayin Galadiman Gozaki (ba a tantance shekarar da ya yi sarauta ba). Sha Madara  shima a matsayin Galadiman Gozaki (baa tantance shekarar da ya yi sarauta ba), Dan Dume Muhammada matsayin Galadiman Gozaki (baa tantance shekarar da ya yi sarauta ba), Abubakar (Abuta) a matsayin Galadiman Gozaki ya yi sarauta daga shekarar1862-1896. Sannan sai Dahiru Abubakar a  matsayin Magajin Dabai daga shekarar 1896-1919.Sannan sai Sarki Yusufu Dahirua matsayin Magajin Dabai daga shekarar1919-1968.Sannan sai Sarki MuhammadYusuf a matsayin Magajin Dabai daga shekarar 1968-1991. Sai Abdullahi Yusuf  a matsayin Magajin Dabai daga shekarar 1992-2006. Sai Sarkin yanzu wato Ahmed Muhammad wanda ya fara sarauta a matsayin Magajin Dabai daga shekarar 2007 zuwa yau. Wadannan Sarakai sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa wannan garin ta bangarori daban-daban musamman abin da ya shafi ilimin addini da kuma lokacin da aka fara na zamani a yankin. Akwai manyan gidaje a garin da suka bunkasa wannan garin.A bangaren ilimin addini akwai manyan Malamai da suka bada gudummawarsa wajen yada ilimi da aiki da shi.

BUKUKUWA A GARIN

Dangane da bukukuwan yankin kuwa, suna gudanar da bukukuwan da suka hada da;na Sallah, Maulidi,kokowa, Dambe da kuma Sukuwa. Da yake tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa gari, mutanen garin Dabai sun dauki noma a matsayin sana’ar da mafi yawansu suke dogara da ita wajen bunkasa tattalin arzkinsu. An yi ittifaki cewa; a duk fadin jihar Katasina,mutanen Kauyen sun fi kowa noman Tumatir. Sannan suna noman da ya hada da na; gyada, rake, auduga, dawa, gero, masara. A bangaren dabbobi kuwa, suna da dabbobin da suka hada da; Shanu, Akuya, Tinkiya, Jaki da Doki.

SANA’O’IN HANNU A GARIN

Daga cikin sana’o’in hannu da suke yi domin dogaro da kansu sun hada da; saka wanda akwai unguwa guda da ake kira da UNGUWAR MASAKA.Akwai fitaccen gida da ake kira da gidan Malam Bala Tanko da suka shahara da wannan sana’a.Hakazalika sana’ar Leda ma tana daga cikin sana’o’insu.Sauran sana’o’in sun hada da; kira, sana’ar tukunya, rini, gini da sauran su.

DALILAN DA YASA GARIN YA BUNKASA

Daga cikin dalilan da ake ganin ya bunkasa garin tun a wancan lokacin zuwa yanzu shi ne nagartaccen shugabanci.Sarakunan garin sun kasance gaba-gaba wajen bi da takurawa dukkan mutumin garin wajen ganin ya koma noma, ko kuma ya kama wata sana’ar hannu da zai taimaki kansa da iyalansa, gidansu da garin baki daya. Misali; a lokacin Sarki Magaji Yusuf ya kasance yana bi gida-gida,unguwa-unguwa yana lura da wadanda suke zaune ba sa aikin komai, ana takurawa musu da karfafasu wajen kama abin yi. Saboda tsananin hora wadanda ba sa komai a garin a lokacin mulkinsaakayiwa Sarkin garin lakabi da ‘Magaji Mai Bulala.’ A lokacin Sarki Magaji Muhammad kuwa, shela ya rika yi cewa; ko dai iyaye su tura ‘ya’yansu bidar ilimi ko kuma su bar yankin gaba daya. Sannan dalili na biyu da ya kawo bunkasar yankin shi ne; sadaukarwa da gudummawar Malamai wajen ilmantarwa da tarbiyyantar da al’umma a garin. Har yanzu akwai manyan gidajen Malamai da akegirmamawa sakamakon gudummawar da suka bayar a garin. Sannan abu na uku da ake ganin shi ne ya bunkasa yankin shi ne; damshin kasa, kyawun kasa da Allah ya yi musu, wacce ta ba da daman yin noma da kuma yada zango da manoma suka rika yi, wanda manoman noma hatsi domin siyar da wasu don samun kudin shiga tare kuma da yin noman da zai ciyar da yankin baki daya. Sannan suna da isasshen ruwan da suke amfani da shi wajen yin noman rani.Sannan har wala yau abu na gaba da ake ganin shi ne dalilin bunkasar yankin shi ne hadin kai. Tarihi ya nuna cewa mutanen garin Dabai sun kasance mutane masu yin aiki tare kai kace ‘yan uwan juna ne. Kuma mutanen garin sun amsa sunan mutanen jihar Katsina da ake ce mata ‘DAKIN KARA.’Abu na gaba da ake ganin yana daga cikin dalilan da ya bunkasa yankin shi ne; kasuwar garin,ta yadda aka rika samun bakin ‘yan kasuwa, sannan ana kawo abubuwan bukata.

ABUBUWAN TARIHI MASU BAN MAMAKI

A lokacin bincikenmu da muka gudanar a wani Kauyen da ake kira da ‘KAHUTU’dake karkashin kulawar garin na Dabai mun ci karo da abubuwan tarihi da suka hada da; kushewar bawan Allah, takun giwa(mai kofatai), matattarar ruwa, kaburbura, da sauran su.

Mai Kofatai: ana kiran wannan dutsenne da ‘TAKUN GIWA’ko kuma ‘MAI KOFATAI’, wurin na cikin Kauyen Kahutu. Tarihi ya nuna cewa; a da kafin yanzu, namun daji ne iri-iri suke zuwa wurin suna hawa dutsen suna hutawa.Sakamakon yawan hawa wurin da dabbobin suke yi yasa idan ka zo dutsen zaka ga sahun dabbobi iri-iri. Har yanzu wurin yana nan, sai dai sawayen ya fara dusashewa. Amma kana iya ganin wasu alamu na sawaye a cikin dutsen da suke da daukar hankali.

Matattarar Ruwa: idan ka isa wurin, zaka tarar da wani rami newanda ya kai tsawon mita 728. Tarihi ya nuna cewa; an yi wani bawan Allah ne da ake yiwa lakabi da Waliy Muhammad Nakahutu, a lokacin da ya rasu mutane sun hadu bayan an haka kabarinsa a kusa da wani dutse, isar wurin ke da wuya da nufin bizne shi, sai aka tarar ruwa ya cika ramin da aka haka domin bizne shi, daga nan sai mutanen suka fasa bizne shi a wurin, suka haka wani rami a gefen wannan ramin sannan suka bizne wannan bawan Allah. Tun daga lokacin, mutanen Kauyen sun tabbatar mana da cewa; ramin ya rika rike ruwa da tara shi har na tsawon shekara, wanda wannan yasa mutanen Kauyen ke amfana da shi. Sannan a cewarsu; a da (banda yanzu) wurin ya rika yin haske musamman a daren Juma’a.Daga nesa kana ganin haskensa fau kamar hasken farin wata.

Kushewar Bawan Allah: sunansa Muhammad, ana masa lakabi da Nakahutu. Mutanen Kauyen sun tabbatar da cewa wannan bawan Allah waliyyi ne. Kuma ya rasu ne akan hanyarsa ta zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji. Shi ne aka je biznewa ruwa ya tsatso a ramin da aka yi niyyar bizne shi.Yana da mata mai suna A’isha Muhammad Nakahutu da kuma ‘ya’ya guda biyu da ake kira da Hassan da Husaini, kuma duk sun rasu ne a lokaci guda, a inda suka aka bizne su a dutse guda. Kabarin matarsa A’isha da ‘ya’yansa Hasan da Husaini suna nesa da shi a saman dutsen da ake kira kushewar bawan Allah. An zagaye su, kuma har yanzu akwai masu ziyarar kabarin na su. Wani abin mamaki shi ne; masu ziyarar idan suka zo suna ajiye kudi domin neman tabarruki a kasan dutsen duka kaburburan na su. Idan ka da ga dutse sai ka ga tarar da kudi. Nima shaida ne, domin na tsinci kudi, na dauka na kuma kashe. An sakawa wannan wuri suna da ‘KUSHEWAR BAWAN ALLAH’ ne sakamakon kaburburan wadannan bayin Allah da yake wurin, kuma ya zama ana girmama su. Kafin rasuwar Waliy Muhammad Nakahutu akwai wata bishiyar tsamiya da ya kasance yana zama karkashinta domin hutawa. Sannan hakazalika har yanzu akwai shaidar Masallaci da ya yi yana gabatar da sallah a wurin.

Exit mobile version