Connect with us

RAHOTANNI

Ziyarar Karin Ilimi Da Daliban Jami’ar Bayero Suka Kai Nijar

Published

on

Haka nan mun ziyarci gidan Sarkin Abzin sai dai kasancewar ba ya gida ba mu sami shiga fada ba. Amma mun yi gaisuwa kuma ‘yanfada sun karba da niyyar isarwa ga mai martaba Sultan, daya cikin manyan sarukuna biyu da ke jamhuriyyar Nijar.
Mun je babbar kasuwar Agadas inda muka sha kallo. Tabbas wannan kasuwa ta yi kama da kasuwar kurmi ta Kano ta hanyar tsarin shaguna da ma irin kayayyakin da ake sayarwa. Haka nan mun je kasuwar dabobi ta a-ci-da-kofato inda muka ga rakuma da shanu da tumaki irin na mutanen Nijar. Na lura galibin tumakansu balamaye ne masu tsawo da girma fiye da irin na kasar Hausa. Shannunsu kuma jajaye ne masu tsawo wanda ake kira da Azawad.
A ranar Laraba mun ziyarci dausayin Dabaga, wani dausayi da ke can Arewa da garin Agadas. A wannan hanya mun wuce wurare masu yawan da duwatsu da kwazazzabai. Galibin duwatsun da ke kan hanya sun kasance sandstone, wani dutse mai taushi mai karbar ruwa. A wasu wuraren duwatsun wuta (ignous rocks) sun hudo kai amma galibi sun ratattake sun janza (metamorphoses) daga yanayinsu. A haka mu ka cigaba har mu kai ga kwogin Telwa. Shi Telwa wani kogine da ya kasance mai albarka ga wannan al’umma ta Agadas ta inda duk da ba kasafai yake dauke da ruwaba, gurbinsa cike yake da kogin karkashin kasa (groundwater akuifers) mai cike da maramaran ruwa da su ka taru miliyoyin shekaru. A irin wannan yanki al’umma kan yi noman rani ta hanyar tona gajerun rijiyoyi (shallow wells). Don haka wannan yanki na Dabaga da ke kasa da wannan kogi ya kasance yankin mai albarkar noma. Mun sami wurin kore shar ko’ina ka duba sai shuke-shuken kayan lambu da bishiyoyin dabino kai kace ba wannan yanki na Sahara mu ke ba inda ruwan sama ba ya fin milimita dari zuwa da ishirin a shekara.
Washegari Alhamis mun je garin Tchiro mai arzikin gawayi. Shi wannan gawayi wani dutse ne da ake yin makamashi da shi. Kasancewar dutsen kan ci wuta ya kuma samar da zafi mai tsanani ya sanya akan yi amfani da shi don samar da wutar lantaki. A wannan yanki akwai arzikin gawayi jingim cikin kasa wanda ake tonowa don samar da wuta. A kan tono tare da gyara gawayin don samar da wutar lantarki ga yankin Agadas, Agarus da Arlit mai arzikin yuraniyum. Wannan samar da wuta yana bukatar abubuwa uku: gawayi, ruwa da iska. Yayin da arzikin gawayi ya ke fitowa daga Tchiro, ana janyo ruwane daga wani gari mai suna Agarus kemanin kilometer 30 daga mazaunin kamfanin lantarkin wanda ya kasance a inda arzikin gawayin ya ke. A kan janyo ruwa kemanin ton 400 a kowane yini don samar da wuta. Yayin samar da wutar a kan zuba ruwan a cikin wata tukunyar dahuwa (boiler) sa’annan a yi amfani da gawayi don juya wulin (turbin) wanda yake sanya ruwan ya tafasa. Iska kan taimaka wurin zuga gawayin har ya samar da zafi da ya kai kemanin 1000-1200 a ma’aunin selshis (0C). Wannan zafi kan samar da surace (steam) wanda ake juyawa zuwa haske. Wannan haske ya kan kai ma’aunin 660kb. Duk da dai fusahar da ake yin amfani da ita wurin samar da wutar ba ta zamani ba ce domin ana kona makamashi ne yana tashi a iska (hakan zai iya cutar da al’umma da yanayi), amma za ka jinjinawa kamfanin da ke samar da wutar domin kuwa wutar a tsaye ta ke kyam duk tsawon ranukun da mu ka kasance a wannan gari.
Hanyar zuwa garin Tchiro cike ta ke da tsaunuka a dama da hauni. Tsaunuka sun kasance na duwatsun wuta da ake kira da bolcano. Irin wadannan duwatsu an ce sun afku ne a wasu miliyoyin shekaru da suka gabata da aka sami aman dutsen wuta (bolcanic eruption). Alamu na nuna wadannan duwatsu sun tsufa mutuka domin sun fara rugurgujewa, don haka ya na da wahala nan gaba a kuma samun aman wuta a wurin. Duwatsun kan bada sura mai kama da rufin rumbu (cone shape). Da alama wadannan duwatsu wasu sashe ne na Tsaunukan Ayir (Mountain Air) wanda ya kasance wani bango na arewa da hamadar sahara.
A ranar jum’a mun yi ziyara masallacin Elmiskin dake tsakiyar garin Agadas. Masallaci ne mai tsohon tarihi domin an gina shi tun karni na sha biyar lokacin da Shehu Abdulkarim Almaghili ya shigo Agadas bayan fitowarsa daga Tilmisan. Don haka munaiya cewa wannan masallaci sako ne da masallacin birnin Kano wanda Sarki Rumfa ya gina. To amma wani abin sha’awa shi ne yadda wannan masallaci ya kasance a bisa gininsa na kasa da tsarinsa na dauri. Ga shi dai masallaci ne na kasa, amma ya wanzu tsawon karnuka bai rushe ba kuma al’umma bata rusa shi ba. A masallacin mu ka sallaci juma’a sa’annan mu ka gai da liman. Mun so mu hau hasumiyar wannan masallaci wadda itace hasumiyya mafi tsawo ta kasa a wannan duniya. Sai dai ba mu sami ikon hawaba, mun hau dai rubi na farko cikin rubi bakwai da hasumiyar ta ke da shi. Wadannan rubi an ce an yi su ne dai-dai dawafi da sammai bakwai. Haka nanhasumiyyar na da taga bakwai da matatakala dari ba daya daidai da sunayen ubangiji masu tsarki. Hakanan akan fara hawa wannan hasumiya a duke a kare a kaikaice daidai da rayuwar danadam wada ke farawa da wahala da rauni ta kare da wani raunin da zafin futar rai. Hakanan ana riya cewa inda an hau wannan hasumiyya mutum kan sami yafiya da kankarewar zunubansa. Hakika wannan hasumiyya ta na cikin abubuwa mafi jan’hankali a birnin Agadas domin ko ta ina ka daga kai zaka hangeta a wannan gari mai cike da ababan tarihi.
Karshen wurin da mu ka ziyarta shi ne gidan da Henrich Barth ya sauka yayin fitowarsa zuwa kasar Kano Jallabar Hausa. Shi dai Barth Baturen Germany ne da ya zo tsegumi kasar Hausa wajejen 1854 har ya je Borno da Sakkwato da Kano. An ce ma shi ne mabudin Hausa ga Turawan leken asiri. Mun je wannan gida na kasa wanda aka kafawa lamba mai dauke da bayani a cikin harshen faransanci inda aka rubuta cewa “a ranar tara ga Augusta zuwa talatin ga Oktoba Henrich Barth ya sauka a wannan gida a hanyarsa ta zuwa Kano bayan ya fito daga Tripoli.”Abin mamaki shi ne dan achaba ne ya kaimu wannan gida. Kuma da isarmu wata yarinya da ba ta fi shekara bakwai zuwa takwas ba ta ce “sun zo gidan Hanry Barth” ta furta cikin karin harshen turancin faransa. Wannan na nuna lallai tarihi wani abin girmamawa ne a garin Agadas.
Hakika garin Agadas ya burgeni mutuka, kuma na yi burin na koma a nan gaba. Cikin abubuwan da su ka fi birgeni shi ne tsarin gine-ginensu. Duk da akasarin gidajensu ba na zamani ba ne sun kasance masu yalwa.Ga su hanyoyi masu fadi da tsari. Hakanan ba su damu da kwaikwayon al’adun wasu ba wurin gini da kawata garinsu. Ko ina ka gifta za ka ga zannen Agadas (Agadas Cross) wanda wata alama ce ta tarihin wannan al’umma. Haka kuma Agadas ya zamto gari daya da ya isa darasi ga manyan garuruwan Hausa: Katsina, Zariya da Kano inda duk an lalata da watsi da kayan tarihi. Na tabbata wadannan garuruwa duk da suna da tarihi daidai da,ko ma sama da na Agadas ba su iya jerawa da Agadas wajen alkinta kayan tarihinsu. Ga su dai su mutanen Agadas sai sheda mana su ke cewa ‘komi daga Kano yake zuwa mana’, shi ko bakano sai cewa ya ke ban ga Kano ba sai a Agadas. Duk da kasancewar garin nada tsadar rayuwa hakan bai dameni ba domin idona ya ga abinda yake muradi kuma da ma bahaushe yace yayin biyan bukata ai rai ba a bakin komai ya ke ba, balantana ‘yan sulala da ka na iya samunsu ko wane lokaci. Hakika alkaryar Agadas wata kyauta ce da Madaukaki ya yi a cikin tsakiyar Sahara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: