Ziyarar Likitoci Sinawa A Saliyo Za Ta Ceci Rayukan Dimbin Mata
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Likitoci Sinawa A Saliyo Za Ta Ceci Rayukan Dimbin Mata

byCMG Hausa
2 years ago
Likitoci Sinawa

Birnin Freetown na Saliyo ya karbi manyan baki a jiya Litinin, wato tawagar likitocin kasar Sin, da za su taimakawa kasar yaki da cutar sankarar bakin mahaifa. 

Sankarar bakin mahaifa, cuta ce da ta zama abar tsoro a tsakanin mata la’akari da yadda take wahalar da su da kai wa ga asarar rai a karshe. A cewar hukumar lafiya ta duniya, a shekarar 2020 kadai, cutar ta yi sanadin mutuwar mata 342,000 daga cikin kimanin 604,000 da aka yi kiyasin sun kamu da ita a shekarar a duk fadin duniya. Kuma kaso 90 cikin dari daga cikinsu, mata ne na kasashe masu matsakaici da karancin kudin shiga.

  • Don Tinkarar Hauhawar Farashi Ake Neman Shiga Tsarin BRICS

Likitocin za su gabatar da kwarewarsu a fannonin bincike da kula da gano cutar ta sankarar bakin mahaifa, tare da horar da takwarorinsu na kasar.

Irin wadannan tallafi da kasar Sin kan bayar ga kasashen Afrika a kai a kai ne dalilin da a koda yaushe na kan kira kasar a matsayin wadda ta san ya kamata kuma sahihiyar aminiya ga kasashen Afrika. Har kullum taimakon kasar Sin ga al’ummar Afrika, taimako ne irin na ’yan uwantaka, na sanin ciwon dan uwa, haka kuma taimako ne na kai tsaye da mutane za su amfana da shi. Zuwan likitocin, tabbas ba karamin taimako zai bayar ba, wajen ceton dimbin rayukan mata da ma karfafawa matan gwiwar zuwa ana duba su tun kafin cutar ta ci karfinsu.

Baya ga haka, yadda tawagar likitocin suka tashi musamman suka zuwa Afrika, zai kara zaburar da mahukuntan nahiyar wajen kara kula da lafiyar mata. Wani abu dake burge ni da kasar Sin shi ne, baya ga mayar da hankali kan kulawa da jama’arta, tana bayar da muhimmanci na musamman ga lafiyar mata. Tuni ta dauki dabarun yaki da wannan cuta mai kisa ta hanyar gudanar da bincike da kulawa, har da samar da rigakafi ’yar kasa.

Hakika akwai dabaru da darussa da dama da likitocinmu na nahiyar Afrika za su iya koya daga takwarorinsu Sinawa. Fatan ita ce, kwalliya za ta biya kudin sabulu, kana kasar Sin ta fadada wannan taimako zuwa sauran kasashen nahiyar domin ceton karin rayuka. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Buhu 116 A Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Buhu 116 A Jihar Kano

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version