Ziyarar Shugaba Xi A Turai Ta Kara Bayyana Muradin Sin Na Ganin Tabbatuwar Zaman Lafiya A Duniya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Shugaba Xi A Turai Ta Kara Bayyana Muradin Sin Na Ganin Tabbatuwar Zaman Lafiya A Duniya

byCGTN Hausa
1 year ago
Xi

Yayin da shugaban Sin Xi Jinping ke ci gaba da ziyara a kasar Faransa, ya tattauna da manema labarai tare da shugaban kasar Emmanuel Macron, a jiya Litinin. Shugaba Xi ya bayyana wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa, kuma daga cikinsu akwai wadanda suka fi jan hankalina su ne:

Na daya, a shirye Sin take ta hada hannu da Faransa wajen amfani da wasannin Olympics a matsayin dandali na wanzar da zaman lafiya a duniya. Ba sai an fada ba, duk mun san yanayi na hargitsi da duniya take ciki yanzu haka, kana mun san irin rawar da wasanni ke takawa wajen ingiza hadin kai da zaman lafiya tsakanin mabanbantan al’ummomi. Hakika kasar Sin ta yi kyakkyawan tunani na amfani da wasannin na duniya, wajen ingiza sulhu tsakanin kasa da kasa. Matasa su ne kashin bayan kowanne al’umma. Don haka, idan ana amfani da dandamali irin na Olympics wajen yayata bukatar zaman lafiya da kyawawan akidu, a nan gaba za a samu al’umma mai fahimta da ganin mutuncin juna, wadanda za su rayu cikin zaman lafiya.

Na biyu, Sin na goyon bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine. Tabbas kamar yadda shugaban ya fada, maimakon ingiza rikici ko tallafawa rikicin kamar yadda wasu ke yi, kasar Sin ta kasance mai kira da warware rikicin ta hanyar tattaunawa. Tarihi ya nuna cewa sulhu ba ya samuwa sai da tattaunawa, don haka ya dace bangarori masu ruwa da tsaki da ma wadanda ke ci gaba da ruruta wutar rikicin, su mayar da wuka kube, su rungumi mafita mafi dacewa ta hawan teburin sulhu domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Na uku, kasar Sin na kira da a dakatar da bude wuta a rikicin Palasdinu da Isra’ila tare da kafa kasashe biyu. Sanin kowa ne Sin ta kasance gaba gaba wajen kiraye-kirayen tsagaita bude wuta ga rikicin. A matsayinta na babbar kasa, har kullum tana goyon bayan samar da zaman lafiya a duniya, tare da kasancewar murya ga masu rauni. Dadewar da aka yi ana takkadama tsakanin bangarorin biyu ya tabbatar da cewa, idan ba samar da kasashe biyu aka yi ba, ba za a taba samun zaman lafiya ba, kuma rikici na iya bazuwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

A ganina, hadin gwiwa tsakanin Sin da Faransa, zai taka rawa wajen dakile fito na fito da wasu kasashe ke neman tadawa tsakaninsu da Sin, haka kuma zai dakile bullar kananan rukunonin da ake kafawa da zummar dakilewa ko matsawa wata kasa lamba. Ziyarar shugaban Sin a Turai, ta nuna cewa, Sin ba ta neman kafa rukunin kawaye, sai dai rugumar kowa da kowa domin inganta dunkulewar kasashen duniya, ba tare da wariya ba, domin samar da zaman lafiya mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta

Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa'adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version