Connect with us

RAHOTANNI

Ziyarar Shugaban APC Ta Haifar Da Ficewar Shekarau Zuwa APC

Published

on

A kokarin karkare maganar ficewar Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, Gwamna Kano Dakta AbdullahiUmar Ganduje tare da shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Kwamared Adams Oshiomole sun ziyarci gidan Shekarau wanda ke Titin Mundubawa domin karkare shirye shiryen ficewar tasa da safiyar Juma’ar data gabata.
Tawagar Shugaban Jam’iyyar ta APC na Kasa Adams Oshomle, Abdullahi Umar Ganduje OFR tare da ‘yan Majalisar Dattijai guda biyu na Jihar Kano, Shugabannin Jam’iyya, ‘yan majalisar dokoki na Jihar Kano tare da ‘yan majalisar zartarwa duk suna cikin tawagar data isa gidana Sardaunan na Kano. Kamar yadda aka tabbatar tawagar shugaban Jam’iyyar ta Kasa sun sauka afilin sauka da tashi na filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Shugaban Jam’iyyar na kasa yazo Kano ne domin ziyatar Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau a gidansa na Mundubawa. Inda suka tattauna a dakin taro Na Zainab dake fadar ta Mundubawa da misaln karfe 10:00 na safe, kamar yadda aka sani rade radin ficewar Malam Ibrahim Shekarau daga Jam’iyyar PDP ta haifar da yamadidin cewar Shekarau ya kammala shirye shiryen ficewa daga Jam’iyyar PDP tare da dubun dubatar magoya bayansa. Saboda haka wannan ziyara ta shugaban Jam’iyyar ta APC Adams Oshomole tare da wasu gwamnoni ya share hanyar aniyar tsohon gwamna Shekarau na ficewa daga Jam’iyyar ta PDP zuwa Jam’iyya mai Mulki ta APC.
Adams Oshiomole ya bayyana cewa aduk wata hadaka idan masu kaunar ci gaba suka hadu dole makiya ci gaba su tsere, a nawa tunanin Shekarau yafi wasu mutane da yawa idan dai batun ci gaba ake a kasa. Yace Malam Ibrahim Shekarau na cikin sahun wadanda suka samar da Jam’iyyar APC, yana cikin wadanda suka samar da cigaban Kasar nan wanda muke da kyakkyawan tunani iri guda.
Saboda haka ina mutukar farin ciki dana kasance a wannan wuri, wanda na ziyarci tsohon kwamared wanda ya aminta da ayyukan cigaban kasa, na san kyakkyawar aniyarka ga makomar siyasa da kuma tattalin arzikin kasa tare da cigaban ta, wannan hadaka na cikin matakin farko na cigaban da muka aminta dashi, saboda haka mun zo nan domin karawa juna karfi domin ciyar da kasarmu gaba, inji Oshiomole.
Da yake gabatar da nasa jawabin Malam Ibrahim Shekarau ya fara godewa shugabancin Jam’iyyar ta APC wanda suna nuna muhimmancinsa wanda aka baiwa irin wannan kyakkyawar kulawa. Ina mtaukar godiya ga shugaban Jam’iyya da Kuma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje saboda nuna abokata da kusa wannan ziyara ta siyasa. Yace ina tabbatar maku da cewa zamu ci gaba da kasancewa tsintsiya daya ma daurinki guda.
Shekarau y akuma bayyana Kwamared Adams Oshiomole da cewa tsohon aminin mune inji Shekarau, yace rarihi ne ke maimaita kansa, ina godiya kwarai bisa kasancewa ta a irin wannan matsayi ayau cikin Jam’iyyar APC. Haka kuma ya bayyana danganatakarsa da Gwamna Ganduje inda yace tun lokacin da na bar Jam’iyyar APC muna da kyakkyawa danmgantata da Gwamna Ganduje da kuma sauran jama’arsa. Wannan kuma ya biyo bayan irin tarbiya da kuma al’adarmu bama raina mutane a kowa ne hali muka tsinci kanmu.
Saboda haka Malam Ibrahim Shekarau ya tabbatarwa da wadanan muhimman mutane da ma al’ummar Kano baki daya cewa wannan hadaka zata haifar da kyakkyawan ci gaba ga Jihar Kano da ma Kasa baki daya, musamman kansacewa muna da abubuwa da dama da muka hadu akansu musamman tarbiya, siyasa da kuma kaunar jihar Kano da kasa baki daya.
Shima ana sa Jawabin Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shi yafi kowa farin ciki a wannan rana, musamman wanna hadaka ce da muka yi domin ciyar da Jihar Kajo da kasa gaba, yace wannan hadewa ta Shekarau da Jam’iyyar APC tazo har abada. Ganduje yace ni da Shekarau muna abubuwa iri guda musamman yadda ako da yaushe muke amatsayin abokan juna, ni na fi kowa farin ciki kasancewar yanzu muna cikin Jam’iyya guda da Shekarau, dukkan mu mun aminta da cigaban kasa.
Saboda Haka Gwamna Ganduje yace duk wasu abubuwa tsakanin Gwamnatin da shekarau za’a tattauna su, ya tuna shekarau cewa yana cikin wadanda suka samar da Jam’iyyar APC, amma mun san ka bar Jam’iyyar ne sakamakon wasu abubuwa wanda son zuciya na Gwamna Kwankwaso.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: