Ziyarar Zulum: An Mutsuttsuke ’Yan Gudun Hijira 20 Wajen Rabon Kayan Abinci

Majiya mai tushe ta bayyana cewa kimanin mutane 20 ne suka mutu, wadanda mafi yawan su mata ne da kananan yara, a wani tarnatsatsin turereniyar karbar tallafin kayan abinci da kudade, a sa’ilin da Gwamna Zulum ya kai ziyara a sansanin yan gudun hijirar jihar Borno da ke zaune a Diffa ta jamhuriyar Nijar, ranar Litinin din da ta gabata.

Bugu da kari kuma, kimanin mutum 12 ne suka samu raunuka a lokacin wannan ziyara wadda Gwamna Babagana Zulum ya kai a matsugunin, majiyar ta ce “muna da adadin mutane 20 wadanda suka mutu ta dalilin turereniyar”. Kamar yadda wani ma’aikacin kiwon lafiya; na kungiyoyin agajin gaggawa ya tabbatar, tare da karin hasken cewa mutum 12 sun gamu da raunuka daban-daban.

Wannan turnutsitsin ya faru ne a cibiyar al’adun gargajiya ta MTC da ke birnin Diffa, daya daga cikin wuraren da aka tsara Gwamna Zulum zai kai ziyara.

Wanda Gwamna Zulum ya shirya gudanar da kai wannan ziyara a jamhuriyar Nijar tare da raba kayan agaji da tallafi ga jama’ar jihar Borno, wadanda matsalar tsaron Boko Haram ta tilasta musu kauracewa yankunan su.

Wani ganau a lokacin wannan ziyara tare da raba kayan abinci da na masarufi hadi da kudin, ya shaidar da cewa, a rana ta farko, an gudanar da raba kayan cikin tsanaki, amma daga bisani; rana ta biyu, al’amarin ya rikide zuwa gogoriyo da turereniyar, a lokacin da dubun-dubatar jama’a suka samu labarin raba kayan- lamarin da ya jawo wurin ya yi cikar kwari.

Majiyar ta kara shaida mana kan cewa Gwamnan Diffa hadi da Kakakin majalisar dokoki, sun ziyarci asibitin da aka ajiye gawawakin wadanda suka mutu tare da duba wadanda suka samu raunukan, duk da ba su fitar da wata sanarwar manema labarai ba.

Wannan lamarin dai ya jawo masana tofa albarkacin bakin su tare da fashin baki kan cewa wannan karara ya nuna jama’ar suna cikin mawuyacin hali, yunwa da ganin uwar bari.

Exit mobile version