Zlatan Ibrahimovic ya kafa tarihin zura kwallaye 500 a raga, yayin karawar kungiyar AC Milan da Kungiyar Croton yadda ta doke kungiyar da ci 4-0 ta kuma kasance a saman teburin gasar seria A na Italiya da maki 49.
Dan kwallon, an haifeshi a 3 Ga Oktoba, 1981. Dan asalin kasar Swedin Wanda ke taka leda a gaba. Dan Wasan ya zama futacce cikin ‘yan wasa Wanda yake daya daga cikin manyan masu buga gaba a cikin shekaru 20 da suka gabata.
A halin yanzu adadin kwallayen da Ibrahimovic ya ci a kungiyoyin da ya haskawa da kuma kasar sa ta Sweden sun kai 501.
Bambancin Tuchel Da Pochettino A PSG
Ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Monaco ta je har...