Wata muhimmiyar ganawar sirri da ta gudana tsakanin jami’an gwamnatin jihar Katsina da kuma tawagar ministan ma’aikatar harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta Najeriya na nuni da cewa zata haifar da da mai ido dangane da kafa kamfanin zaka a garin Funtua.
Wannan ganawa na da nufin samar da wani kyakkyawan yanayi ta fuskar kasuwanci da kuma zuba hannun jari ga ‘yan kasuwa na waje da na cikin gida, ta hanyar samar da katafaran kamfanin zaka da za a kafa masana’antu a jihar Katsina.
Da take jawabi ga manema labarai a Katsina ministan harkokin masana’antu da kasuwanci da zuba jari Maryam Katagum ta bayyana irin dangantakarr da take tsakanin ma’aiktarta da kuma gwamnatin jihar Katsina, inda ta ce daga cikin abubuwa da za su duba a jihar akwai abubuwan da gwamnatin Katsina ta samar musamman a garin Funtua domin asassa mana’antu
Ta kara da cewa za su kai ziyara a wajan da gwamnati ta samar domin ganewa idanunsu abubuwan da ke kasa da suka hada da layin wutar lantarki da hanyoyin sufuri.
“Acikin wannan tattaunawa da muka yi, mun yi bayani akan tsarin aikin da zamu yi, ba wai duba wuri kawai ba, zamu sanya masu tuntuba domin yin abinda ya kamata da kuma kyakyyawan nazari akan wannan aiki, kuma muna bukatar masu ruwa da tsaki a cikin wannan shiri, wanda hakan zai baiwa masu zuba hannun jari damar zuwa jihar Katsina” inji ta
Haka kuma ta kara da cewa acikin wannan tattaunawa da suka yi sun amince cewa za su ziyarci wannan katafaran wuri da gwamnatin jihar ta samar domin kafa masana’anta a garin Futua domin gani da ido ya fi labari.
Sai dai a nashi jawabin mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ya bada tabbacin goyan bayan gwamnatin Aminu Bello Masari akan baban shiri, inda ya ce sun shirya tsaf domin bada gudunmawar da ake bukata.
Haka kuma ya kara da cewa sun ji dadi matuka dangane da wannan tattaunawa da suka yi da ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, inda ya ce wannan ne karo na farko da suka taba ganawa da wata mininta har tsawo awa biyu akan mahimman abubuwa da suka shafi jihar Katsina.
“Mune muka fara kai ziyara har ofishinki, amma tun daga wancan lokacin babu abinda ya faru sai bayan wata shida, amma yanzu gashi mun fara wannan aikin da zai iya canza yanayin tafiyar tattalin arzikin jihar Katsina, muna da fatan cewa katafaran kamfanin saka na Funtua wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi sai zama mai amfani a garemu” inji shi
Alhaji Mannir Yakubu ya kara da cewa gwamna Aminu Bello Masari ya amince da bada kadada 140 domin a gudanar da wannan aikin na gina kamfanin saka na Funtua, ya ce sai daga bayan suka lura cewa wannan aikin yana bukatar baban wuri wanda yanzu haka sun kara mika kokon baranmu domin karin wani filin, inda ya ce suna da fatan cewa za a samu karin so sai.
Haka kuma ya godewa ministan da ‘yan tawagarta bisa nuna damuwar da jihar Katsina da kuma wannan muhimmin aiki da suka sa gaba na samar da katafaran kamfanin Zaka a garin Funtua wanda ya ce cikin karamin lokacin anyi abubuwa da dama.