Zuba jari a tashoshin ruwa zai yi matukar bunkasa bangaren bakin takun kasar nan tare da karin haraji ga gwamnatin tarayya. Shugabar hukumar kula da tashoshin ruwan Nijeriya (NPA), Hadiza Bala-Usman ita ta bayyana haka lokacin da take kira a kan akwai bukatar kara farfado da bangaren tashoshin ruwa da ke fadin kasar nan. Shugabar hukumar NPA ta bayyana cewa, kayayyakin more rayuwa da gwamnati ta gina a tashoshin da kadarorin da aka samu a karkashin shugabancinta sun yi matukar bunkasa tashoshin bakin ruwan Nijeriya wanda ya kara kudaden shiga a bangaren tashoshin jiragen ruwa.
“Dokin cimma burikanmu, muna bukatar kara samun manyan jiragen ruwa wadanda za a yi amfani da su a tashoshin,” in ji ta.
Ta kara da cewa, domin samun damar aiwatar da ayyuka yadda suka kamata a dukkan tashoshin jiragen ruwa, hukumomi sun yi kokarin ci gaba da fadada kayayyakin aiki, domin kara inganta gudanar da ayyuka.
“An gudanar da wannan kokari ne domin tabbatar da dukkan tashoshin bakin teku guda shiga su kasance suna aiki yadda ya kamata a kowani lokaci.
A nasa bayanin, ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, babu wanda yake musun cewa, tashoshin jiragen ruwa suna da matukar mahimmanci ga banfaren tattalin arziki, a lokacin da aka saka dokar hana zirga-zirga a cikin wata uku da suka gabata, a wannan lokacin ne aka gane mahimmancin bangaren tashoshin ruwa a cikin kasar nan.
“A yanzu haka, gwamnati tana kokarin bunkasa sauran fannonin tattalin arziki domin rage dogaro da bangaren mai da gas, mun san rawar da bangaren tashoshin jiragen ruwa suke takawa a cikin kasar nan musamman ma a bangaren farfado da tattalin arziki a cikin wannan gwamnati.