Connect with us

MURYAR TALAKA

Zubar Jini A Zamfara

Published

on

Ana ci gaba da kashe talakawan Zamfara ba kaukatawa. Alkalumman baya-baya na nuna, ‘yan ta’adda da mariddai sun ci karfin gwamnati! Gwamnatin tarayya wadda alhakin tsaro ke kanta, ta zama kamar babu ita. A gabanta kullum sai an kashe mutane a kauyukan Shinkafi,Zurmi da Dansadau.
Rahotanni na nuna yanzu kananan hukumomi da dama a Zamfara na karkashin barayi, inda suke dora ma kauyawa haraji na miliyoyi ko su biya, ko a kawo masu hari. Allah kadai yasan wadanda suka biya a boye. Ga alama salon rubuta takarda a tura ma gari ko kauye cewa su biya kudin fansa ko a kawo masu hari na nuna koluluwar lalacewar al’amurra a jihar Zamfara dama kasarmu Najeriya.
Tun a da muna mamakin yadda ake danfashi ya fi karfin gwamnati, yanzu hart a kai mun fara amincewa, kila fa danfashin ya fi karfin raunannar gwamnatin Najeriya mai takama da bada tsaro.
Akwai fa kauyen da ‘yan fashi suka shiga tun karfe tara na safe suna cin karensu babu babbaka, har karfe 5 na yamma amma babu jami’in tsaro daya da ya kai ceto! Wannan fa a Najeriya ne, inda daya daga manufofin gwamnatin shi ne tsare rayuka da dukiya, amma a banza.
Idan an kashe su , ko an kore su daga kauyukansu sun koma sun tare a gine-ginen makarantun gwamnati, sai gwamnatin tarayya ta tura hukumar NEMA da katihu,barguna da abinci a kai masu.
Wai barayi, ‘yanfashi da batagari su fi karfin gwamnati? Kai wannan abin mamaki ne.
E, gwamnati ta gaza, ta kasa, babu wani abu ga alama da yai saura. Yanzu lamari ya koma kan talakan Zamfara.Kodai ya ci gaba da kallo, ana kashe shi daya bayan daya, ko kuma ya dauki matakin da ya dace . Matakin ‘yan sintiri, baida tasiri, matakin siyasa ya fi tasiri. Domin danbanga baida kudade ko lasisin da zai sai makamin da zai yaki danfashi,gwamnati ita keda wannan, don haka ita ce , yakamata Zamfarawa su tursasa domin a dauki abin da ke faruwa a Zamfara da muhimmanci.
Kasashen da talaka ya waye a siyasance, dauke wutar lantarki kawai na iya tasiri a zabe mai zuwa, amma banda Najeriya. Wannan yasa an raina talakan ,ba a dauke shi a bakin komi ba. Duk da irin mutanen da kullum ake yankawa, a kashe su a Zamfara, amma wai wani daga jihar ya mike yana fadin “mai daraja gwamna”? wai ya yi kokari? Wai don Allah mike damunmu? Wane irin kokari ake a Zamfara? Ko mun daina daratta ran dan adam sam a Najeriya ne? Mutane ne fa ake kashewa a Zamfara, ba kwari ba, amma har yau zuwa yanzu abin bai ci kujerar kowa ba tun daga matakin tarayya zuwa karamar hukuma. Kullum sai an kashe mutum a Zamfara, amma babu jami’i daya da ya taba cewa na yi murabus bada ni ba cikin wannan tafiyar. Wani abin lalacewa ma, jihar an bar ta ba gwamna sai mukaddashin gwamna. Wannan wane irin zalinci ne? Ta yaya jihar dake cikin jihohi mafi muni a kashe mutane da mayar da wasu ‘yan gudun hijira, a ce kuma gwamna baida lokacin zama cikinta wai sai mukaddashin gwamna Ina gwamnan yake? Me yake a inda yake? Shin aikin kungiya ya fi ye mai aikin da yai rantsuwa a kansa?
Abin da ake jihar Zamfara zai nuna maka yadda shugabanni da ‘yan siyasa suka raina talakan Najeriya, don sun san cewa bai iya komi. Kuma sun san cewa waya da katin waya da Naira dubu goma zaka ba shi kawai ranar zabe ya sauya ra’ayinshi. ‘yancinsu na nuna rashin jin dadinsu game da kisan da barayi ke masu, shima aka hada baki da gwamnatin jihar Zamfara da jami’an tsaro aka dakile, inda aka dakile zanga-zangar gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar.
Yanzu fa duk irin cin kashin da ake a Zamfara, ranar zabe, mutum daya zai ce ga wanda za a zaba, kuma mutanen su je su zabe shi.
Haba ‘yan Zamfara, ba ku ga yadda mutanen Binuwai sukai da gwamnansu ba? Koda karya ce, idan har gwamnan Binuwai Samuel Ortom zai ce matasa sun tursasa mai ya bar APC, to ku mi kuka iya da gwamnanku? Ba kune kuka zabi ‘yan majalisar jihar ku ba? Koko dora masu ku akai da tsiya? In dai kuna fadi a ji, kuna da ikon akan ‘yan majalisarku, to yakamata ku kira su ku ce kun basu awa 24 su tube Yari.
Koko kun zabe barin jinin Zamfarawa ya tafi a banza a wofi? Ku girgiza siyasar Zamfara ku nuna kun san ‘yancinku. Ku kori azzalumai masu wasa da rayukanku. Mi ake da mulkin da baida amfani , mulkin da kodayaushe barawo ko dan fashi na iya aika ka lahira. Meye ribarku a Zamfara da za ku bari a kawar daku daga doron kasa?
Gwamnatin tarayya ta gaza a harkar tsaron Zamfara Me yasa ake ci gaba kashe-kashen in har ana wani abu? Zamfarawa ku nuna ‘ya’yane ku cire siyasa kui waje-rod da gwamnatin da dauki rayukanku ba bakin wata tsiya ba. Baku da tsaro to mi yai saura? Idan kuma kuka ci gaba da hira a shafukan jaridu da tarukan kungiyoyi ba tare da daukar kwakkwaran matakin siyasa ba, to kuwa za ku dandana kukanku. Domin za ku dasa wata siyasa ta dolanci wadda za a dauki lokaci mai tsawo ba a fita daga cikinta. Ku kawo karshen gwamnatin karya, gwamnatin yaudara, gwamnatin da ta kasa kare ku. Bata da wani amfani, kui waje da su. Gwanma ku fito su sa jami’an tsaronsu su kashe ku da ku bari ‘yan banza barayi na kisanku. Ku farka domin alkalumma na nuna babu wani abinda wadannan tarkacen za su yi maku.
FARANSA
Faransawa wadanda ked a tarihin gwagwarmayar juyin-juya sun nuna ma shugaban kasarsu Emmanuel Macron cewa, ba za su lamunci wani yai wasa da ‘yancinsu ba, inda suka tilasta ma shi korar Aledander Benalla mutumen da aka bankado yana muzguna ma ‘yan zanga-zanga, sannan majalisar dokoki ta kada ma gwayanke kauna wadda ya shad a kyal. Da fatan Nijeriya za mu koyi wani abu daga siyasar Faransa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: