Abdullahi Muhammad Sheka" />

Zuki-Ta-Malle Ce Batun bullar Cutar Covid-19 A Kano – Gwamnatin Jiha

Hukumar Lafiya ta Jihar Kano, ta lura da wasu labaran kanzon kurege da ke yawo tsakanin al’umma ta hanyar sadarwar zamani, wanda ke bayyana cewa an samu bullar cutar Covid-19 a Jihar Kano.

Wannan labarin kanzon kuregen da ake kafar sadarwar  CNN da BBC ta dauka wanda ke bayyana cewa, dalibai biyu na Jami’ar Bayero sun kamu da cutar, wanda aka ce Gwamnatin Kano ta tabbatar da samun cutar ta Covid-19.
Don haka, wannan labari ba gaskiya ba ne, karya ce kuma wani shiri ne na son zuciya da aka kulla, domin tayar da hankulan al’umma.
A kokarinta na warware wannan labarin kanzon kurege, Hukmar Lafiya ta Jihar Kano ta bayyana cewa, babu wani labarin bullar wannan cuta ta Covid-19 a Jihar Kano.
Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya bukaci dukkanin kungiyoyi da daidaikun jama’a, su yi watsi da irin wancan labarin na kanzon kurege, wanda karya ce kawai zunzurutunta tare da jita-jita maras tushe, ballantana makama da ake yadawa domin tayar da hankulan al’umma.
Dakta Tsanyawa, ya kuma shawarci al’umma da su rungumi dukkanin wasu matakan kare kai daga dukkanin wasu cututtuka, ta hanyar wanke hannu tare da nisanta kansu daga shiga cikin dukkanin wani cunkoso. Sannan kuma su yi kokarin sanar da Cibiyoyin lafiya duk wata alamar bullar irin wannan matsala, kamar yadda Jamai’ar Yada Labaran Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Hadiza Namadi ta bayyana wa LEADERSHIP A YAU.

Exit mobile version