Daga Muhammad Maitela,
Darakta Janar a hukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta Nijeriya reshen jihar Borno (NYSC)- Birg. Janar Shu’aibu Ibrahim, ya ce cikin shekaru biyu, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da umurnin were sama da naira miliyan 400 don tallafa wa hukumar wajen kula da jin dadin daliban masu aikin bautar kasa a fadin jihar.
Babban jami’in hukumar ya bayyana haka ranar Litinin a birnin Maiduguri a bukin yaye dalibai kimanin 269 da suka samu kwarewa a fannin yanayin kasa (Soil Doctors and Edtension), yayin da kuma ya yaba wa Gwamnan bisa wannan namijin kokari wanda ya ce ya cancanci yabo da godiya.
A hannu guda kuma, shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron yaye daliban, ya jinjina wa Gwamna Zulum dangane da wannan kokarin.
Ya ce, Gwamnan ya yi abinda ya dace a yaba masa dangane da wannan babbar hobbasa ce wajen kyautata alakar gwamnatin sa da hukumomin gwamnatin tarayya da ke aiki a jihar, wanda hakan ya dace matuka.
Sanata Lawan ya kara da cewa duk da kalubalen da Gwamna Zulum ya sha fuskanta a kokarinsa na dawo da al’amurra kan turba a jihar tsakanin shi da yan ta’adda, hakan bai sanya gwiwarsa ta yi sanyi ba balle ya razana a wannan manufa tashi ta kokarin inganta rayuwar al’ummar jihar Borno.
A jawabinsa, Babban Sakataren hukumar kula da ci gaban yanayin kasa ta NALDA, Mista Paul Ikonne, a taron ya bayyana Gwamna Zulum daya daga cikin jajirtattun gwamnoni nagari wadanda ba su da abokin burmi a fadin kasar nan.
Ya ce babban abin a yaba ne irin wannan kokari na Gwamna wajen samar da ingantaccen filayen noma a karkashin shirin samar da ayyukan noma ga matasa a jihar.
Bugu da kari, wadannan matasa wadanda su ka samu horo na musamman, kumanin 269 wadanda kuma su ka fito daga kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar Borno. An horar da su hanyoyin binciken yanayin kasa a karkashin shirin samar da matasan manoma ta hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumar NALDA da ma’aikatar kula da dabbobi da bunkasa kiwon Kifi a jihar.
A bayaninsa, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa akwai bukatar kwararru a wannan fanni na yanayin kasa domin sake farfado da ayyukan noma a Nijeriya.
A hannu guda kuma, Zulum ya yaba da kokarin gwamnatin da ta gabace shi a karkashin jagorancin Sanata Kashim Shettima, wanda ya ce, gwamnatinsa ce ta dora harsashi mai inganci a fannin ayyukan noma a jihar