Muhammad Maitela" />

Zulum Ya Karade Kauyuka 28 A Kwale-kwale

Ranar Lahadin da ta gabata ne, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya gudanar da rangadi ta hanyar kai ziyarar gani-da-ido, inda ya karade wasu kauyuka 28 wadanda matsalar tsaron Boko Haram ta tilasta al’ummarsu barin yankunan a baya-bayan nan.

Wadannan kauyukan, wadanda su ka shahara a ayyukan noma da ke kusa da tafkin Alau, wato tafki na biyu a jihar Borno, yankin da ya fuskanci hare-haren mayakan ISWAP da Boko Haram, lamarin da ya jawo wa jama’ar yankin arcewa daga garuruwansu zuwa matsugunan ’yan gudun hijira.

Mafi yawan ’yan gudun hijirar na cigaba da gudanar da rayuwarsu a sansanonin ’yan hijira na birnin Maiduguri ne.

Gwamna Zulum ya kai ziyarci kauyukan a kwale-kwalen sojoji, sannan kuma sojojin Nijeriya da ke yaki da matsalar tsaron Boko Haram, wadanda su ka hada da sojojin ruwa, sojojin kasa da na sama su na yi ma sa rakiya.

Kafin wannan lokacin, bayanai sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun sha mamaye yankunan Tafkin Alau, wanda ya ke da tazarar kilomita 20 daga birnin Maiduguri, kuma wannan tafkin shi ne ya ke samar da mafi yawan kayan marmari da kifin da jama’ar birnin ke bukata, kuma ita ce madatsar ruwa mafi girma.

Haka kuma, biyo bayan sake ’yanto yankunan daga hannun Boko Haram, Gwamnatin Jihar Borno ta fara shirye-shiryen farfado da noman rani a Tafkin na Alau.

A wata sanarwar manema labarai, mai daule da sa hannun Malam Isa Gusau, jami’in hulda da jama’a a ofishin Gwamna Zulum, ya bayyana cewa wannan ziyara Zulum zuwa kauyukan shi ne, “domin sake farfado da ayyukan noman rani a yankin, saboda saukaka yanayin rayuwar mazauna kayukan.

”Mun kawo wannan ziyarar ne saboda sake farfado da hanyoyin bunkasa ayyukan noman rani, a wannan Tafki na Alau.

“Kuma a masaniyar mu, akwai kauyuka 28 wadanda matsalar ta shafa, wadanda ke sansanin yan hijira, kuma za mu duba yuwuwar sake dawo da yan uwan mu, maza da mata. Inda kuma ya yaba da kokarin sojojin Nijeriya a aikin samar da tsaro a yankin”.

Malam Isa Gusau ya ce, kafin haka, Gwamna Zulum ya ziyarci cibiyar rarraba ruwa a madatsar ruwa ta Alau, domin tantance kayan aikin da aka tanada domin aiwatar da shirin.

“Haka kuma Gwamna ya ziyarci hukumar kula da renon itatuwa da ke Maiduguri, a wanda ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar Borno ke kula da shi,” ji Gusau.

“Sannan kuma Gwamnan ya yaba da yadda aikin ke gudana, a karkashin kulawar shugabanin cibiyar kula da renon iraruwan da ma’aikatan ma’aikatar albarkatun ruwan sha”. Ya bayyana.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin sake gina gidaje 500, wadanda maharan Boko Haram ta ruguza a yankin Kawuri da ke karamar hukumar Konduga, a jihar.

Wannan furucin ya fito daga bakin Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, a ziyarar da aikin da ya kai, a garin Konduga ranar Lahadi.

Bugu da kari kuma, Babagana Zulum ya sake bayyana cewa, gwamnatin sa ta kammala sake gyara karin wasu gidaje kimanin 250.

Haka zalika kuma, ya kara da cewa, aikin sake ginin gidajen zai taimaka wajen dawowar al’ummar yankunan wadanda yanzu haka su ke zaune a matsugunan ’yan gudun hijira.

Har ila yau, Zulum ya umurci injiniyan da ke kula da aikin da su yi kokari wajen kammala aikin kafin 15 ga watan Yuni mai zuwa.

“Sannan kuma, a lokacin da mu ke kokarin sake dawo da al’ummar garin Kawuri zuwa garuruwan su, za mu mayar da su zuwa garin Umarari. Kuma muna so jama’ar su gudanar da ayyukan su na wannan daminar bana, cikin watan Yuni,” ya tabbatar.

 

Exit mobile version