Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kwashe yinin ranar Litinin wajen aikin raba kayan tallafi a garuruwan Ngoshe, Warabe da Pulka, da ke karamar hukumar Gwoza, a kudancin Jihar Borno.
Kafin nan, Zulum ya yada zango a Ngoshe, domin sanya ido kan aikin raba tallafin kayan abinci da kudi Naira miliyan 24 ga kimanin mabukata 1,200, yan gudun hijira wadanda suka dawo garuruwan su daga Pulka da Maiduguri.
Gwamna ya jagoranci mika wa kowane magidanci buhun masara mai nauyin 50kg, buhun dawa 50kg, da na wake mai nauyin 25kg, shinkafa 12.5kg, man girki lita 5, da sauran kayan alatu tare da Naira 20,000.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan tallafi ne wanda za a ci gaba da aiwatar dashi don karfafa gwiwar yan hijirar da suka koma yankunan su, kana kuma hakan zai taimake su wajen samun damar ci gaba da ayyukan su na noma domin dogaro da kansu.
A hannu guda, Zulum ya kai ziyarar gani da ido ga aikin samar da kayan karatu a makarantar firamarin garin Ngoshe wanda hukumar bayar da ilimin bai daya a jihar ke gudanar dashi tare da kokarin sake bude makarantar nan da mako biyu masu zuwa. Wanda aikin ya kai matakin kaso 95 cikin dari na kammala.
Baya ga wannan kuma, ya duba aikin ginin cibiyar kiwon lafiya mataki na farko a garin na Ngoshe, wanda ya bukaci dan kwangilar ya tabbatar ya kammala aikin a daidai lokacin da aka kulla yarjejeniya da shi, domin bunkasa kiwon lafiyar al’ummar yankin.
Daga garin Ngoshe, Gwamna Zulum ya zarce zuwa garin Warabe, shima a karamar hukumar Gwoza inda ya kai ziyarar gani da ido a aikin gina gidaje 350 wadanda gwamnatin jihar ke gina wa, wadanda Boko Haram suka rusa.
A karshe Gwamna Zulum ya ya karkare ziyararsa a garin Pulka, wanda a can ya duba yadda aikin ginin makarantar sakandiri ta zamani a garin.