Gwamna Babagana Zulum na Borno, a ranar Juma’a a Maiduguri, ya umurci ‘yan Nijeriya da su yi addu’a ga sojoji, masu sa kai na kungiyar Hadin gwiwar kungiyoyin farar hula, wadanda suka bace da wadanda suka yi gudun hijira sakamakon tashin hankalu, a yayin da suke bikin Kirsimeti.
“Yayin da nake yiwa kowa fatan bikin Kirsimeti cikin lumana, farin ciki da albarka, ina rokon dukkan mu da muyi tunani kan yadda jami’an tsaro, mafarautan cikin gida da ‘yan banga ke yin bikin Kirsimeti a cikin daji, suna farautar Boko Haram sannan kuma maharan suma suna farautar su.
“Ya dace mu ma muyi tunani kan yadda iyalan wadannan dakaru da masu sa kai ke yin bikin ba tare da iyalansu da ‘yan uwansu ba, ” in ji gwamnan a sakon Kirsimeti.
“Yin tunani a kan yanayin ‘yan uwansu zai tayar da hankalinmu don sake sadaukar da kai ga yin addu’o’i ba tare da tsayawa ba don samun zaman lafiya da kuma tallafawa jami’an tsaro dake yaki da masu tayar da kayar baya ta hanyar samar da bayanai masu dacewa ga jami’an tsaro,’ ‘in ji shi.
“Za mu ci gaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro, musamman wadanda suka nuna kwazo.
“Za mu yaba kuma mu ba da lada, kuma a inda ake bukatar tayar da jijiyoyin wuya za muyi hakan, duk a madadin ‘yan kasa da muka rantse za mu kare hakkinsu. ” in ji Gwamna Zulum.
Da Dimi-diminsa: Buhari Ya Sauya Shugabannin Rundunonin Tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da murabus din shugabannin...