Daga Muhammad Maitela,
A kwanan sa na uku na ci gaba da ziyarar da a Damasak, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya gabatar da shigar da yayan yan gudun hijira kimanin 1,163 zuwa makaranrar firamare a kokarin sa na bunkasa ilimi matakin farko.
Kananan yara daga kananan hukumomin Guzamala da Abadam a arewacin jihar Borno, wadanda suka shafe dogon lokaci a sansanonin yan gudun hijira tare da mahaifan su biyo bayan yawaitar hare-haren Boko Haram a yankunan su.
Gwamna Zulum ya yi kira ga iyaye da cewa su kai yaransu makarantu, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokari wajen inganta cibiyoyin ilimin da habaka su zuwa matakin da zai bai wa daliban cikakkiyar damar koyon ilimin boko da na ilsamiyya.