Daga Muhammad Maitela,
A kokarinsa wajen saukaka wa jama’ar da matsalar tsaro ta shafa a yankunan karkara, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar a garin Damasak, shalkwatar karamar hukumar Mobbar a arewacin jihar, inda a ranar farko ya kaddamar da tallafin kayan noman rani ga manoma 1,200 don bunkasa ayyukan gona da wadata jihar da abinci.
A rana ta biyu a garin na Damasak, Zulum ya gudanar da raba kayan abinci ga yan gudun hijira kimanin 10,000, wanda kowane mutum daya ya samu tallafin buhun shinkafa mai nauyin 25kg, buhun wake 25kg, buhun masara 25kg tare da lita biyar na man girki don saukaka musu kuncin rayuwa.
Gwamna Zulum ya ziyarci yanki tare da rakiyar Sanata mai wakiltar arewacin jihar Borno a zauren majalisar dattawa kana kuma dan asalin garin Damasak, Hon. Abubakar Kyari, wanda ya raba injinan bayin ruwa, takin zamani, iraruwa, magungunan kashe kwari hadi da kyautar naira 5000 ga kowane manomi domin bunkasa noman rani da yankin ya shahara dashi.
Ya ce wannan daya daga cikin manufofin Gwamna Zulum, wanda a kowane lokaci burinsa shi ne sake tsugunnar da jama’a tare da tallafa musu don samun hanyoyin dogaro da kai wanda hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da jama’a ke fuskanta tare da dogaro da kai.
A nashi bangaren, Gwamna Zulum ya bukaci manoma a garin Damasak, da sauran yankunan jihar da cewa su yi kokari wajen habaka aikin noma wajen noma abinci da dogaro da kai wanda hakan zai taimaka wajen rage dogaro daga kungiyoyin jinkai.