Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
A ci gaba da kokarin sa na saukaka yanayin matsin rayuwar da al’ummar jihar sa ke ciki, Gwamna Babagana Zulum, a wannan karon ya ziyarci karamar hukumar Bama, tare da gudanar da raba tallafin naira miliyan 200 da kayan abinci ga magidanta yan gudun hijira 70,000 maras karfi.
Yan gudun hijirar wadanda suka kwashe tsawon lokaci matsalar tsaron Boko Haram ta jefa su cikin halin ni’yasu da tilasta musu kauracewa yankunan su; babu noma balle sana’o’in dogaro da kai, a wannan karon sun ci gajiyar jinkan gwamnatin Zulum domin sake farfado da rayuwa kamar yadda take.
Har wala yau, an gudanar da raba kudaden tare da kayan abinci a manyan cibiyoyi guda uku da ke shalkwatar karamar hukumar Bama.
Yayin da aka raba wa mata 40,000; kowace daya jakar sikari biyu tare da gudumawar naira 5,000 wanda ya Kama naira miliyan 200.
A hannu guda kuma, magidanta 30,000 kowane daya ya samu tallafin buhun shinkafa, masara tare da katon na taliya.
Da yake jawabi ga dandazon jama’ar da suka ci gajiyar tallafin, Zulum ya bayyana cewa, “Mu na tare daku dangane da duk halin da kuke ciki na rayuwa, kana kuma rokon ku, kowa ya dage da addu’ar samun zaman lafiya a jihar mu.” In ji Zulum.