Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da ware naira biliyan 12 wajen biyan tsuffin ma’aikata 4,862 hakkokin da su ke bin jihar tare da hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin jihar daga 2013 zuwa 2017.
Kafin hakan, a watan Satumba da Yulin 2019, Gwamna Zulum ya bayar da umurnin ware naira biliyan 3 wajen biyan tsuffin ma’aikatan jihar 1,684, wadanda mafi yawan su kananan ma’aikata ne wanda suke bin bashi a 2013 zuwa 2019.
Zulum ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da mika cak na kudin ga wasu daga cikin tsuffin ma’aikatan, ranar Talata a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Maiduguri. Ya yi karin haske da cewa sun biya bashin ne ta hanyar bashi da suka karba daga Zenith Bank.
A hannu guda kuma ya shaidar da cewa duk da wadannan naira biliyan 12 ba za su biya bashin hakkokin da tsuffin ma’aikatan ke bin jihar ba, wanda adadin su ya doshi 5,000 da aka tantance a wannan karon. Saboda hakan ya roki wadanda sunan su bai fito a cikin wadanda za su ci gajiyar wadannan naira biliyan 12 ba, ya bukaci su kara hakuri saboda gwamnati ta na aiki wajen ganin ta biya su hakkokin nasu nan kusa.
Da ya ke karin haske dangane da al’amuran fanshon, Gwamnan ya sanar da cewa daga Mayun 2019 zuwa yau, akwai kimanin korafe-korafe 770, wanda kimanin 650 ne suka samu dubawa kuma a halin da ake ciki yanzu suna cin gajiyar fanshon su face kawai suna jiran ariyas din su kuma nan kusa za a biya su.