Zulum Ya Yi Wa Sabon Shugaban Sojojin Nijeriya Fatan Alheri  

Zulum Sojoji

Daga Muhammad Maitela,

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya taya sabon Babban Hafsan sojojin Nijeriya, Manjo Janaral Farouk Yahaya murnar mukamin shugaban rundunar sojoji na kasa, tare da shiga sabon ofishin nasa ranar Jummu’a.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan a sanarwar manema labarai bai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, ya ce zabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wajen nada kwamandan “Operation Hadin Kai” mai shalkwata a jihar Borno ya dace tare da kasancewa yar manuniya dangane da yadda fadar shugaban kasa ta damu da halin da arewa maso gabas ke ciki na rikicin Boko Haram.

“Haka kuma, nada Janar Yahaya, dama ce ga Nijeriya wajen ci gaba daga inda aka tsaya na yaki da matsalar tsaron, ganin yadda kusan dukan manyan Hafsoshin sun yi aikin tsaro a jihar Borno tare da samun cikakkiyar kwarewa da masaniya kan yaki da Boko Haram da na ISWAP. Wanda bisa wannan nake taya sabon shugaban rundunar sojojin Nijeriya murna, wanda ko shakka babu wannan zabi da shugaban kasa ya yi wa Manjo Janar Farouk Yahaya abin a yaba ne, saboda kafin nada shi yana zaune a Maiduguri a matsayin kwamandan da yake jagorantar yaki da matsalar tsaro, sannan mataki ne da ya tabbatar kan cewa shugaban kasa ya himmatu sosai a yaki da matsalar tsaron da ta addabi arewa maso gabas dama kasa baki daya.”

“Wannan babban abin burgewa ne, ta la’akari da yadda dukan su- marigayi Babban Hafsan sojojin, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da shugaban ma’aikatan shalkwatar tsaron Nijeriya, Janar Leo Irabor, an nada su ne bisa ga kwarewar da suke da ita a matsayin kwamandojin cibiyar yaki da Boko Haram, wadda ke da mazauninta a jihar Borno.”

“Har wala yau kuma, shima Babban Hafsan sojojin sama na Nijeriya, ya rike mataimakin kwamandan rundunar yaki da Boko Haram da ke jihar Borno, kana shima Hafsan mayakan ruwa ya zauna a jihar Borno, wanda dukan su suna da kwarewa dangane da yaki da matsalar tsaro. Hakan ya nuna shugaban kasa ya damu da halin da arewa maso gabas take ciki, dangane da rikicin da ya kwashe shekaru 12 yana gudana, wanda ya lakume dimbin rayuka tare da tilasta wa dubun-dubata kauracewa yankunan su baya ga kona garuruwan da Allah ne kadai ya San adadinsu.” In ji Zulum.

A karshe, Zulum ya ce, “Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar Borno su ci gaba da addu’a da bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro cikakken goyon baya, sannan a namu bangaren, a matsayin gwamnatin jihar Borno, insha Allah za mu ci gaba da bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro, yan sa kai hadin gwiwa da kokari wajen sauke nauyin da ya hau kanmu domin nemo hanyoyin da suka dace wajen samun dawamamen zaman lafiya a fadin jihar Borno, arewa maso gabas da Nijeriya baki daya.” Ta bakin Gwamna Zulum.

Exit mobile version