CRI Hausa" />

Zumuncin Dake Tsakanin Sin Da Afirka Na Kara Bayyana A Dukkan Fannoni

Yayin da kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar cutar COVID-19 a cikin kasarta, yanzu haka annobar na ci gaba da yaduwa a sassan duniya, inda take illa ga bangarorin rayuwa daban-daban, har ma da hasarar rayuka. A dai-dai lokacin da ya dace duniya ta hada kai wajen ganin bayan wannan annoba, a hannu guda kuma wasu kasashe na kitsa abubuwan da ba su dace ba, tare da nuna yatsa ga wasu kan asalin wannan cuta.

A baya-bayan nan, hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa, masana sun yi ittifakin cewa, cutar numfashi ta COVID-19 na da asali da dabba, kuma ba wani ne ya kirkiro ko ya samar da ita a dakin bincike ko a wani wuri ba.
Haka kuma, a matsayinta na hukuma mai kwarewa a fannin kimiya, masana na tunanin cutar ta samo asali ne daga dabba, “watakila akwai ta a jikin jemaga, amma har yanzu ba a gano yadda dan-Adam ke daukar cutar daga jikin Jemagen ba.”
Ta kara da cewa, hakika akwai dabbar dake yada wannan cuta daga Jemagu zuwa jikin dan-Adam. A don haka, ta yi alkawarin cewa, WHO tana maraba da dukkan kasashe, da su goyi bayan kokarin da ake yi na gano asalin kwayar cutar, tana mai cewa, kungiyoyi da dama, ciki har da masanan kasar Sin, suna can suna kokarin gano asalin wannan kwayar cutar.
Amma abin takaici shi ne, duk da wannan shaidu da muhimman bayanai da aka sanarwa duniya, wasu kasashen yammacin duniya na kokarin siyasantar da wannan batu, tun boye kuskuren da suka tafka game da gazawarsu ta daukar matakan dakile cutar a kasashensu.
A yayin da cutar ke ci gaba da yin illa a nahiyar Afirka, kasar Sin ta tabbatar da zumuncin dake tsakaninta da nahiyar, inda a baya-bayan nan, kasar Sin ta ba da taimako na gaggawa na yaki da wannan annoba ga ’yan uwa kasashen Afirka, ta hanyar tura tawagogin ma’aikatan lafiya da kayayyakin yaki da wannan annoba, zuwa kasashen Afirka a wani mataki na zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama’a.
Haka kuma, a ’yan kwanakin nan, tawagar ma’aikatan lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Burkina Faso ta kai ziyara a asibitoci da dama dake kasar, domin yin musayar ra’ayoyi da masanan sassan kasar.
Shi ma rukunin kamfanin kera motoci na GAC dake birnin Guangzhou na kasar Sin, ya baiwa Najeriya gudummawar kimanin dala dubu 51, don taimakawa kasar wajen yaki da cutar COVID-19. Duk wadannan sun kara tabbatar dadadden zumuncin dake tsakanin sassan biyu. Komai wahala komai dadi.
Sai dai yayin da kasashen duniya ciki har da kasar Sin ke kokarin kawar da wannan cuta, ta hanyar raba fasahohi da kwarewa gami da taimakon kayayyakin kiwon lafiya har ma da ma’aikata zuwa kasashe daban-daban na duniya, babban darektan hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi nuni da cewa, kawo yanzu hukumar ta samu rahotanni sama da mutane miliyan 2 sun kamu da cutar. Kuma yanayin yaduwar cutar a yankunan duniya sun sha banban.
Ya ce, wani labari maras dadi shi ne, duniya ba za ta koma kuma ba za ta taba komawa kamar yadda take a baya ba. Da ma masu iya magana ke cewa, “Ai ba a bari a kwashe dai-dai”. Don haka, ya zama tilas mu yi kokarin samar da duniya mai koshin lafiya, da kwanciyar hankali da tsaro, wadda kuma za ta kara shirya tinkarar abubuwa na ba-zata. “Ga ni ga wane, aka ce ya ishi wane tsoron Allah.” (Ibrahim Yaya)

Exit mobile version