Daga Abdullahi Usman, Kaduna
Tun bayan cin zaben Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, al’ummar Jihar Kaduna ke ta murna da farin ciki ganin cewa Allah ya kawo wanda zai canza Jihar Kaduna ta zama kamar Dubai. Domin kusan dukkan al’ummar jihar na da kyakkyawan fata ga Malam saboda irin ayyukan da ya yi lokacin da ya zama ministan babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai shekaru kusan uku da kafuwar Gwamnantin Malam Nasiru El-Rufa’I, mutanen Jihar Kaduna jikinsu ya fara sanyi ganin cewa ba a rabu da Bukar ba, wai an haifi Habu.
Al’ummar jihar sun fara tunanin cewa anya kuwa Gwamna Malam Nasir ya kamo bakin zaren. Ganin yadda jihar har yau take cikin koma baya ta wajen samar da abubuwan more rayuwa da kuma ciyar da jihar gaba.
Yayin da al’ummar ke wannan tunanni a wancan bangare, sai kuma ga wasu zunubai da Malam Nasiru ya yi wa al’ummar jihar wanda za a dauki lokaci ba a manta da su ba.
Ayyukan Ci gaba
Bangaren ayyukan, wanda ta wannan hanyar ne ake ganin gwamna El-Rufa’I ya kware. Domin ta nan ne zai iya mayar da jihar Dubai. Amma abin da al’umma ke kallo yanzu shine bisa dukkan alamu Darfur Jihar Kaduna ke niyyar komawa, ba Dubai ba.
Misali tun watan Nuwamban 2016 ne aka tashi al’ummar da gidajensu ke bakin titi a Unduwar Dosa, Karamar Hukumar Kaduna ta arewa, amma har yanzu ba a yi komai ba a wannan aiki. Haka babban titin garin Kaduna, wadda gwamnatin Alhaji Muktar Ramalan Yero ta ba da aikin fadada shi. Shi ma tun da aka kammalashi shekara daya Kenan ba a ci gaba da yin kashi na biyu na wannan aiki ba. Ballantana a je ga kashi na uku.
Sannan babbar gadar Kawo, duk a Karamar Hukumar Kaduna ta arewa, wadda Gwamnatin jiha ta yi alkawarin canza ta. Ita ma har yanzu shiru ake ji.
Gina manyan otal guda biyu da Gwamnati ta santa tallar kusan shekaru biyu da suka wuce. Shi ma har yanzu ba a kara jin duriyar maganar ba. Haka batun gina babban shagon sayar da kayayyakin masarufi na aka ta da gidan wasa na yara da ke dab da gidan Gwamnati don gina wannan shago, shi ma ba labari.
Cire Sarakunan Gargajiya
Gwamna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’I, ya kori Hakima da Dagattan Jihar Kaduna har 4,776 daga kan kujerunsu a cikin watan Junin da ya gabata. Hakan ya biyo bayan shirin da Gwamnatin ta ke da shi ne na mayar da Hakimai da Dagattai zuwa yadda suke kafin shekarar 1999.
Sai dai mutane da daman a ganin wannan abu da Gwamnatin ta yi, ya taimaka sosai wajen ragewa Gwamnan farin jinni a wajen al’umma. Dama tuni suke ganin Gwamnan a matsayin wanda bai damu da masarautun Gargajiya ba. Kuma suna kallon abin da aka yi wa Mai martaba Sarkin Zazzau lokacin rantsar da Gwamnan a watan mayun 2015 da kuma hana Sarkin na Zazzau shuga gonar Olam da aka yi a makon da ya gabata lokacin da shugaba Buhari ya zo don kaddamar da ita da cewa duk wasu abubuwa ne da Gwamnan ke yi don rage darajar masarautu a jihar.
Sayar Da Gidajen Gwamnati
Wani batun kuwa shine na sayar da gidanjen Gwamnati da ke jihar, wanda adadinsu ya kusan dubu biyu. Wanda kusan dukkanin gidajen ma’aikatan Gwamnati ne ke zaune a cikinsu. Tuni aka siyar da wasu daga cikin wadannan gidaje kuma har yanzu wasu na nan a kasuwa ana jiran masu saye.
Mafi yawan mutanen jihar ba su yarda da sayar da wadannan gidaje ba. A cewarsu gidajen na taimakawa jihar wajen tsugunar da ma’aikatanta da kuma saukar da wasu baki idan jihar ta yi. Sannan sayar da su ba zai fid da jihar daga halin da ta ke ciki ba.
Daga cikin gine-ginen da Gwamnati ta sanya a kasuwa akwai gidajen ma’aikatan shari’a, kamfanin Tumatur na Ikara, kamfanin magunguna na Zariya da kuma kamfanin Citta na Kafancan, duk mallakar Gwamnatin Jihar Kaduna.
Mutuwar Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa
Wani abu da ake kallon Gwamnan da shi shine yadda wani lokacin bai cika tattauna magana ba ya ke furta ta. A taron da ya yi a ranar asabar din da ta gabata na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, gwamnan ya yi wata magana, in da ya roki ’yan jam’iyyar da su yafe masa idan har ya yi musu laifi. Ya ce “Ku sanar da ni idan na yi muku laifi. Zan durkusa in nemi gafararku. Amma idan ba ku sanar da nib a, kuka ce za ku yi fada da ni, to ku je ku yi ta yi. Amma ku tambayi Umaru Musa da Jonathan, dukkansu shugabannin kasa ne. sun yi fada da ni, amma daya yana kabari, daya kuma yana Otueke (Kauyensu).
Wannan kalami na Gwamnan ya fusata mutane da daman gaske. Musamman wadada suke kallon marigari Umaru Musa a matsayin mutumin kirki da ya taimaki jihar Katsina na Nijeriya. Don haka ita kanta wannan maganar na daga cikin zunuban Malam Nasiru.
Hana Acaba, Bara Da Kuma Tallace-Tallace
Tun hawan Gwamnatin nan bisa mulki ta hana sana’ar Acaba da Bara da kuma Tallace-tallace a kan titunan manyan biranen jihar.
Yayin da wasu ke ganin wannan abin a yaba ne ga wannan Gwamnati, saboda ta kawo gyara ne, don Gwamnatocin da suka gabata sun kasa yin irin wannan abu, amma shi gashi cikin dan karamin lokaci ya zo ya aiwatar da wannan tsari.
Sai dai su kuma wadanda ke yin sana’ar Acaba da tallace-tallace a kan tituna sun bayyana takaicinsu ne kan cewa bas u da wata sana’ar da ta wuce wannan. Saboda da ita suke ciyar da iyalansu, sannan wasu da ita suke biyan kudin makarantar su. Su kuma mabarata na cewa a nemar musu abin yi don ba da san ransu su ke yi ba.
Sai dai abin takaici sama da shekaru biyu Kenan amma har yanzu ba a daina yin Acaba da tallace-tallace a Kaduna ba. Acaba ma yanzu karuwa abin ya ke yi. Domin a baya a unguwannin da suke a wajen Kaduna ne akae yi. Amma yanzu har a kofar gidan Gwamnati ’yan Acaba na wucewa da fasinja. Haka batun ya ke a tallace-tallace. Domin duk in da ake samun dan cunkoson motoci a garin Kaduna, to cike ya ke da masu tallace-tallace.
Yunkurin Rushe Kasuwanni
Batun shirin Gwamnatin na rushe kasuwanni don mayar da su na zamani da Gwamnati ke shirin yi. Kasuwannin sun hada da kasuwar bacci, kasuwar Barnawa, kasuwar Sabon tasha da kuma kasuwar Kurmin Mashi da sauransu.
Wasu na ganin wannan abu ne mai kyau, don zai taimaka wajen kare kasuwannin daga gobara da sauransu. Sai dai kuma ’yan kasuwar na ganin wani sabon salo ne na kwace musu shagunansu daga hannunsu.
Sun kuma bayyana cewa ba za su amince da wannan shiri ba na kwace musu shagunansu da Gwamnati ke shirin yi. Suka ce idan Gwamnati da gaske ta ke yi to ta bas u irin ginin da suke so a yi. Su za su gina da kansu. Abin da ita kuma Gwamnatin ta ki amincewa da shi.
Koma dai me ake ciki, lokaci ya yi da ya kamata Gwamnan Jihar Kaduna ya dawo cikin hayyacinsa. Ya sani cewa mutane ya ke jagoranta kuma ya yi abin da suke so. Domin alamu na nuna cewa zai yi Malam zai nemi tazarce a 2019.