Hussaini Baba" />

ZUREPB Ta Dau Alwashin Rushe Gine-gine Da Akai Ba Bisa Kaida Ba A Zamfara

APC Zuwa PDP

Hukumar tsara birane ta jihar Zamfara watau ( Zamfara Urban and Regional Planning Board ) ta dau alwashin rushe gine – gine da akayi ba bisa kaidaba a fadin jihar Zamfara .

Darakta janar na hukumar  , Sanusi Ahmad Lilo ne ya bayyana haka a takardar da ya sanya mahannu ,  ya rabawa manaima labarai , a Gusau babban birnin jihar Zamfara .

“Daraktan ya kara da cewa , hukumar ZUREPB , a nyita ne bisa doka ta lanba ta biyu a a cikin watan gom na shekara ta 1996 ,domin samun cigaba da  ta tsara gine – gine bisa kaida wannan shine babban aikin ta inji Daraktan .

“Kuma wannan hukumar ZUREPB ita keda hurimin  bada izinin  gine – gine da tsarin yadda za’ayishi ga duk wani mai fili ko gwamnati ko kamfanoni .

“Daraktan Sanusi Lilo , ya bayyana dalilin su da rushe gine – gine guda biya a karamar hukumar Talata Mafara da akayi ba bisa kaida ba .

“Sakamakon saba dokar ,sashi na hamsin da biyu na tsarin mulki doka da masu gine – gine sukayi muka ga babu makawa sai an rushe wadannan gine gige  , mu kabi umarnin dokar na rshe gine – gine  .inji Daraktan .

“Kuma aikin wannan hukumar ZUREPB , babu ruwanta da sanya siyasa a cikin aikin ta , tana aiki ne bisa dokar da takafata na bin kaida wajan gine – gine da tsara birane .

“A karahe Daraktan yayi kira ga alummar jihar Zamfara , da Kamfanoni da Ma’aikatun gwamnati ,idan zasuyi gine – gine koda kwas kwarima ne sai sun naimi izinin wannan hukumar ZUREPB , dan kauce ma sabawa doka hukumar da zai jawo a rushe ginin idan suyi .

Exit mobile version