Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Kwamishinan ilimi na Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Magawata Aliero, ya umurci shugabanin makarantun Sakandare na cikin Jihar da su kai rahoton duk wani malamin makaranta da ya ƙi zuwa wurin aiki akan lokaci.
Alhaji Magawata Aliero ya bada wannan umurni ne lokacin da ya yi, wani taron gana wa da shugabannin makarantun Sakandare da ke a cikin Jihar Kebbi a ɗakin taro na masauki Shugaban ƙasa da ke Birnin-kebbi a jiya. Inda ya ja hankalin malaman makarantun na jihar da su guji ƙin zuwa wajen aiki ko zuwa a makare da kuma tashi kafin lokaci.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin Jihar Kebbi tana bayar da fifiko ga ɓangaren ilimi musamman ilimin firamare da Sakandare. Ya kuma umurci daraktoci da sakatarorin ilimi na jihar da su ɗauki matakin ladabtarwa ga duk malamin da aka samu ba ya gudanar da aikinsa ta yadda ya kamata.
Ita ma Sakatariyar Ma’aikatar ilimi ta jihar, Hajiya Rafa’atu Noman Garba Hammani, ta kari da Jan hakalin shugabanin makarantun Sakandare da cewa baza mu yi ƙasa a gwiwa ba ga bin tsarin da kwamitin ilimin na ƙasa ya fito dashi ba, saboda haka ta ce, duk wanda ya bari aka kama shi da karya dokar da aka shata, toh ya sani cewa za a ladabtar da shi ko ita. Ta ci gaba da cewa ta yi umurni ga shugabannin makarantun da duk wanda ke zama a gidan makaranta kuma ba cikin makarantar ya ke aikinsa na koyar wa ba, toh a tayar da shi ko wanene, kuma a bai wa malamai na makaranta wannan gidan domin malami indan baya da gida toh ba ka tunanin za ya iya tsayawa domin gudanar da aikinsa ta yadda ya kamata.
Daga nan kwamishinan ya godewa shugabanin makarantun ga amsa kiran da yayi mu domin ganawa da kuma irin goyun bayan da suke bayar wa ga ci gaban ilimi a jihar ta Kebbi.