Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Zuwa Ina Ne Mike Pompeo Da Sauran Wasu ‘Yan Siyasar Amurka Suke Son Kaiwa Kasar?

Published

on

Ranar 4 ga watan Yuli, rana ce ta murnar samun ‘yanci ta Amurka. Amma a daidai wannan lokaci, sabbin mutanen kasar da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kowace rana ya zarce dubu 50 a cikin kwanaki uku a jere, kana kuma ana ci gaba da zanga-zangar kin nuna wariyar launin fata, har ma ana kara samun rikici tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sandan kasar. Kamar yadda kafafen yada labaran Amurka suka ce, kara fuskantar matsaloli da dama a ranar samun ‘yanci ta Amurka, yana da alaka sosai da gazawar gwamnati wajen tafiyar da manufofin kasa. Har ma akwai wasu masu amfani da yanar gizo ta Intanet na Amurka wadanda suka zargi Mike Pompeo da sauran wasu ‘yan siyasar kasar tamkar matukan mota masu barci, wato ba’a san zuwa ina ne za su kai kasarsu wato Amurka ba?

Hakikanin gaskiya, Mike Pompeo ba su yi kome ba domin dakile annobar COVID-19 da warware matsalar nuna wariyar launin fata dake addabar Amurka. Amma dangane da batun kasar Sin, yana ta yunkurin shafawa gwamnatin kasar kashin kaji domin cimma muradunsa a bangaren siyasa. A kwanan nan, ya sake zargin jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, a wani yunkuri na bata dangantaka dake tsakanin jam’iyyar da al’ummar kasar baki daya, har ma a cewarsa, wai kasar Sin barazana ce ga duniya.
A matsayin jam’iyya mai mulki mafi girma a duniya, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana nuna himma da kwazo wajen kare muradun jama’ar kasar, wadda ke samun amincewa da cikakken goyon-baya daga wajensu. A yayin da kasar Sin ke kokarin ganin bayan annobar COVID-19 a wannan karo, ko tsoffi, ko jarirai, ko mawadata, ko matalauta, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ba ta bar kowa a baya ba, hatta ma tana iyakacin kokarinta wajen ceto wadanda suka kamu da cutar, al’amarin da ya sake shaida cewa, jam’iyyar tana maida rayuwar al’umma a gaban kome.
Me Mike Pompeo da sauran wasu ‘yan siyasar Amurka za su ce game da hakan? A halin yanzu, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, gami da yawan mamatan sakamakon cutar, duk suna ta dada karuwa babu tsayawa. Muna so mu tambayi Pompeo da sauran wasu ‘yan siyasar Amurka, me ya sa gwamnatin Amurka ta gaza kamar haka wajen shawo kan yaduwar annobar? Ko da gaske ne kuna daukar rayuwar mutanenku da muhimmanci? (Mai Fassara: Murtala Zhang)
Advertisement

labarai