Zuwan Bahaushe Afirka Ta Yamma, Rayuwarsa Da Sana’o’insa (II)

Tare da Dakta Aliyu Ibrahim Kankara 07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Abu ne mai fa’ida a bayyana inda ainihin kasar Hausa ta ke a yau. Gami da mutanen da su ke zaune a cikinta. Mu na iya cewa kasar Hausa ta usulan ta na a Afirka ta Yamma, a farfajiyar da ke a tsakanin Hamada ta Sahara da daujinan da su ke makwabtaka da gabar tekun Atlantika. Don haka ne ma ake kiran wannan yanki da sunan Sudan ta Yamma, watau a turance Western Sudan. Wannan yana a tsakanin Tafin Cadi da bakin Kogin Kwara. Wasu masana tarihi da ilimin harshe kuma sun a cewa wannan kasa ta Hausa ta na a shimfide a tsakanin arewacin Najeriya da kudancin kasar Nijar a dai yankin Afirka ta Yamma. Daga bangaren kudu kuma ta yi iyaka da kabilar Gwari da kabilun kudancin Zariya, daga gabas ta yi iyaka da kasar Borno, daga Yamma ta yi iyaka da kasar Dahormey, a gabar kogin Kwara kenan. Sannan kuma daga Arewa ta yi iyaka da kasar Adar a cikin kasar Nijar.

A yanzu, kasar Hausa ta mamaye jihohi da daman a Arewacin kasar nan, musamman Kano da Katsina da Jigawa da Sokoto da Kebbi da Zamfara. Wani malamin Jami’a ya bayyana cewa ba nan Hausa ta fara ba. Ya ce ta fara daga Azbin zuwa arewa-maso-gabas da tsaunukan Jos. I, hakane.

Kashi fiye da sittin (60) na mazauna kasar Hausa dut Hausawa ne. Amma akwai daga cikinsu wasu kananan kabilu das u ka rabe su su ka zauna tare da su sabili da sha’awar al’adunsu har ma su ka yi masu kaka-gida. Saboda haka su ma sun koma Hausawa da karfi da yaji saboda harshen su da al’adunsu da adabin su duk sun koma na Hausawa. Wadannan kabilu sun hada da Fulani da Barebari da Angas da Nupawa da Yarabawa da karekare da dai sauran su.

Manazarta harshen Hausa a Jami’o’I sun bayyana Hausawa a matsayin wasu al’umma da ke zaune a kasar Hausa tun farko kuma sun a yin Magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa. Ba fa ‘yan kama-wuri zauna’ ba. Wasu malaman Jami’a kuma sun bayyana Hausawa a matsayin mutanen nan da su ka yi kaura daga kasar Hausa zuwa wasu sassa da ke makwabtaka da su ko su ke nesa da su, ko da kuwa ba su yin zance da harshen Hausa din ko kuma yin al’adun su. Su ma wadannan Hausawa ne. Misali, Abakwariga da ke zaune a Taraba ta Najeriya. Hakama wasu Hausawa da ke zaune a kasashen Barkina Faso da Kot Debuwa da Mali. Suma dut Hausawa ne. A cikin wadannan al’ummomi akwai Barebari, Kambarin Barebari, Barebarin Katsinawa, Fulani da Buzaye. Hakazalika, mu na iya nade tabarmar bayanin Mallam Bahaushe da cewa wasu mutane ne da ke zaune a kasar Hausa, kuma al’adunsu da rayuwarsu duka na Hausa ne, kuma addinin Musulunci ya yi kyakkyawan tanaji da tsari a kan su.

Idan mu ka yi la’akari da kasar Hausa mai makwabtaka da Katsina ko kuma lardin Katsinar ita kanta, mu na iya cewa Malam Bahaushe ya shahara tun wajen tsakanin shekarun ko Karni na 17, watau a tsakanin 1641 ya zuwa 1684  watau lokutan mulkin sarkin Katsina Uban Yara  da na dan sa Muhammadu Jan Hazo (1671-84) Katsina ta samu ci gaba sosai ta fuskar tattalin arziki da karatun islama. An samu hadin kai da zaman lafiya, kuma sannan an samu dangantaka mai kyau tsakanin Katsinar da kasashen Kano, Zamfara da Kwararrafa kuma an samu yawan zuwan malaman addini haikan a cikin birnin. Wannan ya faru ne tun lokacin da Adawa, wasu mahalba su ke zaune a wurare kusa da Katsina. Inda su ka fi yawa shi ne Durbi-ta-kusheyi kimanin kilomita 31 gabas da Katsina kusa da Mani da kuma Bugaje  Tuni labari ya gabata cewa dukkan kushewa ko kaburbura masu tarin yawa da girma da ke a Durbi-ta-kusheyi da Muduru da Bugaje na mutanen da su ka yi zama ne a wuraren, tare da sarakunan su. Akwai kabarin Janzama ko Jan Hazo ga mi da wasu da dama a Durbi-ta-kusheyi.  Da ba a samu wadannan kusheyi ba da ba yanda za a yi a tabbatar da ingancin labarin wadannan sarakuna. Babu shakka saboda dadewa an dauka abin kamar tatsunniya ne.

Akwai kuma zancen wasu dodanni da aka yi a daidai wannan lokaci kamar su Gizo, Botorami da sauran su. Akwai kuma zancen Katsi ko kukar Katsi a cikin tsakiyar Durbi-ta-kusheyi da aka ce wata mata ce ana kiranta Katsi ta ke yawan zama a gindin kukar ta na yin ‘yan hidindimun ta (na tsafi, ko ?) Ban da wannan akwai kuma zancen Bagari Jirgo da Buga da Dala da Daka wanda wasu ke tunanin ba a ma yi su ba karya ne. Sun kunshi bayanan wuraren bauta ko zama ko muhimman abubuwan da mutanen wadannan wurare ke aikatawa. Kamar yanda kusheyin Durbi-ta-kusheyi ke nuna lallai an yi wadannan mutane a da, to haka ma wasu tukwane ko makamantan su da akan gino a ko dai gonaki ko a bisa duwatsu ko ma a gidaje, da akan kira ‘kayan mutanen da’ Suma wadannan sun isa su zama shaida cewa an yi mutane a wadannan lokuta kamar yanda aka ce. Bagari Jirgo ya zauna a kofar Sauri a cikin birnin Katsina. An ma ce rafin sagi ya taba lashe gidajen su. Amma labarun Katsi da Buga, wasu sun kira su a matsayin almara. Zancen Adawa ya zo daidai da zancen wasu al’umma da ake kira Sanodawa da aka yi zancen su a Alkur’ani mai tsarki.

Mu na tammanin tarihin Malam Bahaushe ba ya cika sai an kawo zancen kafuwar Katsina da mutanen ta tun zamanin yaki. Hakazalika, a cikin littafin sa, R. Soper ya tabbatas cewa kushewoyin da aka samu a wuraren da ke kusa da birnin Katsina ya nuna cewa akwai jama’a a wuraren tun shekaru aru aru da su ka gabata.  Wadannan Adawa su na da girma sosai kuma ba su da wata sana’ar da ta wuce kere-kere na kayan halbi, su kan shiga jeji su kashe manyan namun jeji. A cikin karni na 15 kewayen birnin Katsina ya cika da jama’a da fatake masu tasowa daga kudu su nufi arewacin Katsinar. Dalilin bunkasar Katsina kenan, wadanda su ka fara kafata su ka shiga kafa kan makeru a inda su ka sami matsugunni suna yin kira. Wannan wata dabara ce da su ka bullo da ita ta maishe da karfe abin amfani ga dan Adam. Sannan a hankali mutanen su ka fara kera makaman yaki da na noma, kamar; bindiga, fartanya, gatari, dagi ko diga, sarka (ta doki), wuka, adda da dai sauran su, su na fansar wa fatake ma su zuwa su yada zango su wuce kasashen Nijar kamar Maradi, Damagaran, ko Yamai, da sauran ayarin manoma. Mutum guda, a bisa kan makerar sa sai ya yi hauya sama da dari ukku (300) Wannan shi ya sanya suma mahalba da manoma su ka kulla kawance da makera, har su ma su ka zo su ka kafa sansanin su.

Za Mu Ci Gaba…

 

Exit mobile version