Zuwan Musulunci Da Sauye-Sauyen Da Ya Kawo A Rayuwar Hausawa (I)

Kafin mu dora yakamata mu dan yi waiwaye cikin abin da ya gabata baya. A baya, mun kalli zamantakewar Hausawa a zamani na tsaka-tsaki, da kuma lokacin da addinin Musulanci ya shigo kasar Hausa, da kuma nau’in wudanda suka kawo addini kasar Hausa. Sannan mun kalli rukunin mutanen da suka karbi addinin a karon farko. Daga karshe mun ga abin da Musulunci ya kara fitowa da Bahaushe a kan lamarin zamantakewa da ire-irenta a musulanci.

Addinin musulunci ya kawo wa Bahaushe canji a zamantakewarsa ta fuskoki kamar haka:

Canji ta fuskar addini

Canji ta fuskar wasu daga cikin al’adun-Bahaushe.

Canji ta zamantakewarsa ta fuskar kwaskwarima.

 

Canji ta fuskar addini, wannan na’uin canjin, canji ne gaba daya, kamar yadda muka ambata a baya. Kafin zuwan Musulunci Bahaushe ba shi da saukakken addini, wato addinin da Alhah ya aiko manzaninsa da shi, sai dai addini irin na bautar dodanni. Ko iskoki, ko kuma gumaka. Amma lokacin da addinin musulunci ya zo wa Bahanshe, sai ya canza akalarsa daga bautawa wadancan abubuwa zuwa bautar Allah shi kadai da ba shi da abokin tarrayya. Da wannan ne Bahaushe ya karkata ga barin bautar wadancan a baben bauta zuwa bautar Allah shi kadai. Don haka ne ma ya kira Allah da sunan Ubangiji, wato Uban duk wani abin bauta in ba shi ba. Domin sunan Allah da Hausa “giji”, shi kuma da tauhidi ya zo wa Balaushe don ya kadaita Allah, sai ya ce Allah shi ne madaukaki abin bautawa da gaskiya bisa cancanta. Da wannan ne yake kiran Allah da Ubangiji.

Canji ta fuskar al’ada. A lokacin da musulunci ya shigo kasar Hausa ya samu Hausawa da al’adu da dabi’u iri-iri, wato masu kyau da marasa kyau, a cikin masu kyan akwai su da zumunci da kyauta, da kara, da al-kunya, da kau da kai, da alheri, da taimakon juna, da gujewa abin kunya, da dai sauransu. Dukkan waddannan abubuwa da muka lissafo ba addini ne ya kawowa Bahaushe ba dama can yana da su, za mu yarda da hakan ta irin kare-karen Magana da hikimar zance da muke da su a harshen Hausa. Misali Bahaushe yana cewa “ gidan zumo ba kasuwa ba ne”. Wato dai gidan masoyi ba kullum ake zuwa ba ta fuskar zumunci kamar kasuwa ba, a’a in an ziyarce shi a kan dauki lokaci kafin a kara zuwa. Haka zalika, yana cewa, zumunci a kafa yake, sannan yana cewa “alheri gadon bacci, ka yar da shi a baya, ka dauke shi a gaba. Da wadannan ‘yan misalai da muka kawo za mu gamsu, muka yarda da cewa, Bahaushe yana wadannan abubawa tun kafin zuwan Musulunci, sai dai shi Musulunci ya kara tabbatar masa da su. A cikin al’adu da dabi’u marasa kyau a zamantakewar Bahaushe da Musulunci ya zo ya hana shi su, sun hada da: Hana shi shan giya da caca, da karya da cin amana, da zina da camfi da bori, da tsafi, da surkulle da rufa ido da dai sauransu. A cikin abubuwan da muka lissafo wadansu daga ciki dama ba halin Bahaushe ba ne tun kafin zuwan Musulunci, kamar zina Bahaushe ya kyamace ta, domin kafin zuwan Musulunci idan aka kama mace ta yi zina bakin kare ake daur mata a kewaya da ita gari ranar kasuwa ba mai auranta. Haka zalika, karya da cin amana ba dibi’ar Bahaushe ba ce tun kafin zuwan Musulunci ya zo ya kara jaddada masa rashin kyan abin.

 

Exit mobile version