Gwarzon Da Ya Kawo Sauyin Kula Da Muhalli A Nijeriya 2024: Balarabe Abbas Lawal
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Da Ya Kawo Sauyin Kula Da Muhalli A Nijeriya 2024: Balarabe Abbas Lawal

byLeadership Hausa
10 months ago
Gwarzo

Ministan Muhalli a Nijeriya, Alhaji Balarabe Abbas Lawal ne ya yi nasarar zama gwarzon shekara ta 2024 na Jaridar Leadership, saboda hangen nesansa da kyawawan manufofinsa da ya aiwatar a ma’aikatarsa ta muhalli, wanda ya yi tasiri da kawo sauyi a ɓangaren kula da muhalli a Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Samar da Kyakkyawan tsari da zuwa da sababbin sauye-sauye waje kula da muhalli, ya bayar da gudummawa sosai kan tsaron kasa da samar da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa, ya sa Balarabe Lawal ya zama fitila a tsakanin takwarorinsa ministoci.

  • Gwamnan Sakkwato Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2025 Na Biliyan 526
  • Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Shirin Ci Gaban Al’umma

Manyan nasarorin da Lawal ya samu sun biyo bayan sabon tsarinsa na yaki da sauyin yanayi da farfaɗo da muhalli a Nijeriya. A Jagorancinsa ya ƙaddamar da wasu tsare-tsare da za su magance matsalolin da suka daɗe ana fama da su a Nijeriya, tare da aiwatar da sababbi da ya da za su magance barazana ga muhalli.

Nasarar da aka samu ta tsaftace Ogoni, lamarin da ya ƙi ci- ya ƙi cinyewa, amma a ƙarƙashin jagorancin Lawal an ga ƙarshensa, ya samu yabo iri-iri daga al’umma daban-daban a ciki da wajen ƙasa kan wannan gagarumin aiki.

Lawal ya samu yabo da goyon bayan al’umma, ta hanyar samun hadin kan masu ruwa da tsaki daga cikin shugabannin yayin kaddamar da ayyukan ma’aikatarsa, kamar tsarin samar da tsaftataccen ruwa a ƙarƙashin Cibiyar Inganta Muhalli a Wiiyakara. Wannan shaida ce ga sadaukarwarsa don farfaɗo da cibiyoyin inganta muhalli da jin daɗin al’umma.

Saurin fahimtar matsalar sare Bishiyoyi, Lawal ya jagoranci rarraba irin Bishiyoyi miliyan 45 a faɗin ƙasa baki ɗaya. Wannan gagarumin ƙoƙarin yaƙi da sare Bishiyoyi, da kuma sake shuka wasu a gandun daji ya taimaka wajen yaƙi da kwararowar hamada da inganta yanayin muhalli.

Shirin ‘Agro-Climatic Resilience in SemiArid Landscapes (ACReSAL),’ shirin ya dawo da darajar kadada 350,000 da ta gurbace. Wannan yunƙurin na nuna kishin al’umma da ƙasa da ake fama da kwararowar hamada da sauyin yanayi.

Fahimtar muhimmancin tattalin arzikin Nijeriya a tafkin Chadi, Lawal ya jagoranci yunkurin ƙasa da ƙasa na dawo da darajar yanayin tafkin. Haɗin guiwa tare da abokan hulɗa na duniya daga EU da UAE da Kanada, ya samar da nasarori masu muhimmanci da suka haɗa da dabarar datsewa da sauyawa ruwa hanya, da kuma samar masa da yanayin kula mai dorewa. Lallai wannan shugaba yana da zimma da ruhin aiki da kuma kishin ganin ingantaccen yanayi mai dorewa a Nijeriya.

Saboda sadaukarwarsa da kula da muhalli, ya tabbatarwa duniya cewa jagoranci nagari zai haifar da sakamako na ban mamaki. Don kishin ƙasa da jagoranci nagari wajen gina ƙasa da ci gabanta mai dorewa, Balarabe Abbas Lawal shi ya lashe kyautar LEADERSHIP na Gwarzon Jagoran Kula da Muhalli na Shekarar 2024.

Lawal ya sanya Nijeriya a babban matsayi mai daraja a ƙasashen duniya kan shirin kula da yanayi da muhalli a ƙawancen duniya (COP28).

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Oluwatobi Ajayi

Gwarzon Shugaban Kamfanoni Masu Zaman Kansu Na 2024: Oluwatobi Ajayi

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version