'Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Garin Jere Sun Yi Awon Gaba Da Mutane
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Garin Jere Sun Yi Awon Gaba Da Mutane

byLeadership Hausa
3 years ago
yan bindiga

A daren Litinin din nan ne wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba suka sake afkawa garin Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wasu mutane.

Majiyarmu daga garin na Jere ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wani magidanci mai suna Hussaini tare da matarsa da ake kira da Hajiyale da ke gidan tsohon Sarkin Jere, marigayi Dakta Sa’ad Usman. Sai dai daga bisani matar ta kubuta.

Har ila yau majiyar ta kara da cewa, ‘yan bindigar sun kuma nausawa Unguwar Salanke, inda suka yi gaba da wani dattijo mai suna Baba Na’ibi Gayya bayan sun harbe wasu jikokinsa biyu, Ahmad da Musa a hannu.

Haka nan akwai wani matashi mai suna Haruna daga Unguwar Iya wanda shi ma ‘yan bindigar sun tafi da shi.

Zuwa rubuta wannan labarin dai ba a san adadin mutanen da aka sace ba. Yayin da garin na Jere wanda aka yi bikin nadin sabon sarkinsa a ranar 23 ga Disambar nan da ta gabata ke ci gaba da alhinin abin da ya faru.

  • Sakon Sabuwar Shekara: Na Yi Iya Bakin Kokarina Wajen Yi Wa Nijeriya Hidima A Mulkina — Buhari

Wannan shi ne karo na biyar da ‘yan bindiga ke shiga garin na Jere suna sace mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
Da ɗumi-ɗuminsa

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

October 1, 2025
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
Da ɗumi-ɗuminsa

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

September 17, 2025
DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
Da ɗumi-ɗuminsa

DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu

September 16, 2025
Next Post
Sabuwar Shekara: Bagudu Ya Bukaci Al’uma Da Su Rungumi Zaman Lafiya

Sabuwar Shekara: Bagudu Ya Bukaci Al'uma Da Su Rungumi Zaman Lafiya

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version