Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin karfafa alakar dake tsakaninta da gwamnatin jihar Kano, domin bunkasa ayyukan more rayuwa da bunkasa ci gaban masana’antu a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, jakadan kasar Sin a Nijeriya, Yu Dunhai, ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci tawagar ofishin jakadancin kasar a ziyarar ban girma da suka kai gidan gwamnatin jihar Kano.
- Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
- 2027: Na Shirya Tsaf Don Yin Aiki Tare Da Peter Obi Don Ceto Ƙasar Nan, Gwamnan Bauchi
Yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbe shi a zauren taron gidan gwamnatin, jakadan kasar Sin ya bayyana yadda al’ummar Sinawa a Kano ke jin dadin gudanar da kasuwancinsu ba tare da tsangwama.
A cewar Dunbai, gwamnatin kasar Sin tana kara inganta alakarta da jihar Kano a fannonin samar da abinci, kayayyakin more rayuwa, ilimi, tare da kasuwanci da gwamnatin jihar.
A fannin aikin gona, wakilin kasar Sin ya yi nuni da muhimmancin samar da abinci a jihar Kano, inda ya ce, jihar da ke da dimbin al’umma kamar kasar Sin, ta cancanci amfani da fasahohin zamani a fannin noma don karfafa samar da dimbin abinci.
A cikin sanarwar, Mista Dunhai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ci moriyar damar da kasar Sin ta samar na zuba jari a Nijeriya na sama da dala tiriliyan 20, domin farfado da ci gaban masana’antu da kasuwanci.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf, wanda ya tarbi tawagar jama’ar Sinawa da hannu biyu, ya kara da cewa, a shirye gwamnatinsa ta ke ta kara himma wajen hadin gwiwa domin ci gaban jihar baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp