A ranar 26 ga watan Agusta, mummunar zaftarewar kasa ta afka wa yankin arewacin kasar Nepal, wadda har ma ta shafi mahadar kan iyakar Gyirong a jihar Xizang ta kasar Sin, wacce ke iyaka da Nepal, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da kuma bacewar dimbin mutane. Hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa manyan gine-gine da dama a mahadar kan iyakar Gyirong sun lalace gaba daya sakamakon duwatsu da laka da suka fado daga tsaunukan da ke kusa. A halin yanzu ma'aikatan ceto suna gudanar da ayyukan gano mutanen da suka bace da ceton rai a wurin da ibtila'in ya faru a Gyirong, kuma ana ci gaba da neman mutanen da suka bace ba tare da sararawa ba a wajen yankin da abin ya faru. Kwanan nan, Malama Chen, mazauniyar birnin Shanghai na kasar Sin, ta rubuta a shafin sada zumunta cewa, ta sami kiran wayar tarho daga ofishin 'yan sanda, inda wani dan sanda ya tabbatar da sunanta da farko, sannan ya tambaye ta game da ziyarar da ta yi a jihar Xizang a kwanan nan, da kuma ko tana da abokan tafiya. A karshe, an tunatar mata cewa, "Wurare da yawa a halin yanzu suna fuskantar ruwan sama mai karfi, don haka ya kamata a magance zuwa wuraren da ka iya fuskantar yanayi mai hadari." A hakika 'yan sanda sun tuntubi Malama Chen don tabbatar da lafiyarta, da kuma neman wasu mutanen da ibtila'in ya shafa ko kuma suka makale. A karkashin bayanin da Malama Chen ta wallafa a shafin sada zumunta, mutane da yawa sun rubuta cewa, su ma sun samu irin wannan kiran kwanan nan. Wani mai amfani da yanar gizo ko Intanet na jihar Xizang ta kasar Sin ya ce shi da dukkan abokansa da ke zaune a gundumar Gyirong sun sami kiran waya, inda aka yi tambaya ko su da iyalansu ibtila'in ya shafe su, kana ko suna cikin Gyirong yanzu. Sauran masu amfani da yanar gizo da yawa sun yi tsokaci cewa, "Tabbas, sauke nauyin yin wadannan kiraye-kirayen waya na da girma sosai" da "Ma'aikata sun kwantar da hankulansu lokacin da aka amsa kiran waya", da kuma "Ina fatan za a amsa duk wani kiran da aka yi." Rayuwa a kasar Sin kamar haka take: idan ka fuskanci matsaloli, kar ka damu, domin akwai wani da zai taimake ka. Kana idan hadari ko ibtila'i ya faru, wani kuma zai damu da lafiyarka. Sai dai, a sauran wuraren duniyarmu, yanayin ya bambanta sosai. A tattaunawar da aka yi da shi, wani masani dan kasar Kanada Jiang Xueqin ya yi tsokaci kan abubuwan da ya gani a Los Angeles na kasar Amurka, a kwanan baya. Yayin da yake halartar wani bikin liyafa a wata unguwa ta masu wadata, ya ga dimibin manyan gidaje wadanda jami'an tsaro masu zaman kansu ke gadi. Sa'an nan a wani yanki na wannan birnin, ya ga tituna cike da mutanen da ba su da matsuguni, wadanda da yawa daga cikinsu suna ta shan muggan kwayoyi. Jiang Xueqin ya ce, "Wannan abin ban mamaki ne kwarai da gaske." Ya kara da cewa, "A daya daga cikin kasashe mafi arziki a duniya, wato Amurka, an bar miliyoyin mutane a baya, ba tare da kulawa da su ko kadan ba." Ya ce, idan an kwatanta da yiwuwar barkewar yaki, ya fi damuwa kan rashin daidaiton zamantakewar al'umma, da lalacewar yanayin cikin gidan wata kasa da ke faruwa sakamakon ra'ayin mutanen yammacin duniya na matukar son kai. A cewarsa, wannan ita ce babbar barazana ga bil'adama. Mutanen kasashen yamma suna goyon bayan ra'ayin barin daidaikun mutane kowa ya tabbatar da kome da kansa, da jaddada muhimmancin 'yancin mutum, kuma suna kallon kasashensu a matsayin "duniya mai 'yanci", sai dai tunaninsu ya kan haifar da matsaloli, misali kadaici da karancin damar samun taimako, da rashin daidaito cikin al'umma, da dora matukar muhimmanci kan karuwar dukiyar wasu mutane maimakon kokarin amfanar da jama'a. Hakika a ganina, ci gaban al'umma ba dole ne ya zama mai bin turbar kasashen yamma ba. Watakila zabi mafi kyau shi ne salo na kasar Sin, wanda ya shafi fayyace ma'anar kalmar "ci gaban al'umma" bisa fahimtar kai, da kokarin gina wata al'umma mai darajanta adalci, inda kowa ke samun kulawa yadda ake bukata. (Bello Wang)
Read moreDetailsSamun Rarar Kudin Ciniki Ba "Laifi" Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin...
Read moreDetails'Yan siyasar kasashen yamma kan karawa batun "rarar kayan da Sin ta...
Read moreDetailsKwanan nan, na karanta wasu bayanai da suka shafi yadda kasar Najeriya...
Read moreDetailsSin ta fara aiwatar da manufar soke harajin fito gaba daya ga...
Read moreDetailsLokacin da ya siffanta abokantakar dake tsakanin Sin da Afirka, babban jami'in kasar jamhuriyar Nijar Ibrahim Manzo Diallo, ya ambaci karin magana da na yiwa wannan rubutu take da shi. Alhaji Ibrahim Manzo Diallo, shugaban kwamitin sa ido kan ayyukan watsa labaru na kasar Nijar, yana halartar taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka karo na 7 a birnin Beijing na kasar Sin. Yayin da nake hira da shi, ya ce yadda shi da dimbin wakilan kafofin yada labarai na kasashen Afirka suka samu gayyata zuwa kasar Sin, don halartar wannan kasaitaccen biki, shaida ce ta zumuntar dake tsakanin Sin da Afirka. Ta yaya za a iya karya babakere da kasashen yamma suke yi ta fuskar aikin yada labarai a duniya? Wannan tambaya ce da Alhaji Ibrahim Diallo ke kokarin neman amsarta. A cewarsa, a baya kasashen yamma sun dade suna shawon kan kafofin yada labarai na kasar Nijar. Amma bayan da kasar Sin ta fara watsa shirye-shiryen rediyo da yaren Hausa da sauran harsunan Afirka, gami da wani salon yada labarai da ya sha bamban da na kasashen yamma, jama'ar kasar Nijar sun rika samun labarai na gaskiya. Hakan ya shaida muhimmancin hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren watsa labarai. Haka zalika, ya kara da cewa, ko da yake kasashen yamma sun dade suna kokarin shafa wa kasar Sin kashin kaji, amma 'yan Afirka sun san wace ce sahihiyar abokiyarsu. Duk wanda ke neman bata huldar dake tsakanin Sin da Afirka, to, ba ya son ganin ci gaban kasar Sin, gami da na kasashen Afirka, in ji shi. Ban da haka, a ganin Alhaji Ibrahim Diallo, akwai alaka tsakanin ci gaban fasahohin yada labarai da zamanantarwar wata kasa. Ya ce, kasar Sin ta yi nisa a fannin kula da sabbin dandamalin yada labarai, irinsu shafin yanar gizo na sada zumunta, da kafar watsa labarai ta kai, da dai makamantansu. Ya ce yana son komawa Nijar tare da fasahohin kasar Sin, don matasa su fahimci cewa, ban da ba da damar yin zage-zage da nuna fushi, sabon dandalin yada labarai na da daraja a fannin raya kasa da zaman al'umma. Alhaji Ibrahim Diallo, ya ce yana fatan ganin matasan kasashen Nijar da Sin sun karfafa cudanya a fannin aikin watsa labarai, ta yadda za su samu karin ilimi, da samar da karin gudunmowa ga ci gaban kasashensu. Kana duk a wajen taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka na wannan karo, na yi hira da Raymond Dokpesi, shugaban kamfanin watsa labarai na DAAR na kasar Najeriya. Ya ce shekarar bana da ta kasance shekarar cudanyar mutane da al'adu tsakanin Sin da Afirka, tana da matukar ma'ana. Ya ce, kasar Sin daya ce daga cikin manyan abokan hulda na kasar Najeriya mafiya samar da tasiri a duniya. A matsayinta na wata babbar kasa mai karfin tattalin arziki, kasar Sin ta nuna wa Najeriya, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka wata sabuwar hanyar raya kai, wadda ta sha bamban da tsohuwar alakar mulkin mallaka da aka samu tsakanin kasashen yamma da na Afirka, da sa kaimi ga sauye-sauyen da ake samu a nahiyar Afirka, musamman ma a fannonin siyasa da tattalin arziki. Yanzu dukkan bangarorin Sin da Najeriya na son ganin an habaka hadin gwiwa da ake yi tsakanin gwamnatocinsu zuwa tsakanin al'ummun kasashen 2, da sanya jama'arsu fahimtar juna da kaunar juna. A kokarin neman cika wannan buri, Mista Raymond ya ba da shawarar gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin Najeriya da Sin, wajen tsara shirye-shiryen bidiyo wadanda za su yi bayani kan alakar Sin da Afirka a tarihinsu. Wadannan mutanen biyu da na yi hira da su, sun zo daga Najeriya da Nijar, kasashe 2 daga cikin kasashe 45 dake nahiyar Afirka masu halartar taron dandalin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka na wannan karo. Duk da haka, maganarsu tana iya wakiltar ra'ayin galibin manyan baki 'yan Afirka da suka halarci taron, wanda shi ne darajanta zumuntar dake tsakanin Afirka da Sin, da sa ran samun karin sakamako a hadin gwiwar bangarorin 2. Sai dai ta yaya kafofin yada labaru na Sin da Afirka za su karfafa hadin kansu a nan gaba? Manyan baki masu halartar taron na wannan karo, sun ambaci yadda za a karfafa hadin gwiwa wajen tsara wasannin kwaikwayon da ake watsawa a wayar salula, da amfani da kirkirarriyar basira ta AI, da cudanya tsakanin manyan jami'ai, da matsasa, da dai sauransu. A zahiri, kafofin yada labarai za su ci gaba da taka muhimmyar rawa a fannin karfafa cudanya tsakanin al'ummun Sin da Afirka, da tabbatar da ci gaban bai daya na bangarorin biyu. (Bello Wang)
Read moreDetailsYau ranar 15 ga watan Agusta ita ce ranar kare muhalli ta kasar Sin karo na 4, haka kuma ita ce ranar da aka fara aiwatar da "Kundin Dokokin Kare Muhalli na kasar Sin" a hukumance. A daidai wannan lokaci, bari mu duba ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni. Bisa alkaluman da aka samar, fadin dazuzzuka ya kai kashi 25% na filayen kasar, kana yawan bishiyoyi da itatuwa da aka dasa a yankunan arewa maso yammacin kasar da arewacinta da kuma arewa maso gabashinta domin inganta muhalli ya kai kashi 40.76%. Fadin kasar da ke fama da kwararowar hamada ya takaita daga kara fadi da eka dubu 343.333 a ko wace shekara zuwa raguwa da eka dubu 666.667 a ko wace shekara. Sin ta zama kasar da ta fi saurin karuwar dazuzzuka a duniya. A yayin da kasar Sin ke samun ci gaban inganta muhallinta, hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ta wannan fanni ma tana bunkasa yadda ya kamata. A watan Yuni na 2026, a taron koli na dandalin tattaunawa kan yanayin muhalli na duniya, an gudanar da wani taron na musamman mai taken "Koyi da kwarewar Sin don inganta yanayin muhalli a gabashin Afirka", wanda ya jawo hankulan jami'ai da masana daga kasashen Afirka da yawa da kungiyoyin kasa da kasa, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kyautata muhalli da samun ci gaba mai dorewa. Mahalarta taron sun kai ga cimma matsaya daya cewa, kwarewar Sin a fannin kare muhalli tana ba da muhimmiyar ma’ana ga matakin da Afirka ke dauka na karkata zuwa hanyar samun bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba, kuma hadin gwiwar Sin da Afirka a wannan fanni na da makoma mai haske. A gefen hamada dake da nisan kimanin kilomita 70 daga Nouakchott, babban birnin Mauritania, Sin da Mauritania sun kafa "Lambun shan iska na gwaji mai amfani da fasahar Sin" mai fadin ekta 4 cikin hadin gwiwa. Masana daga cibiyar binciken muhalli da yanayin kasa ta yankin Xinjiang na Kwalejin nazarin kimiyya ta Sin sun kawo wa wannan yankin kwarewar shawo kan kwararar hamada. Ministan kare muhalli na Mauritania ya yi wa matakin da Sin ke dauka lakabin "juyin-juya-hali a bangaren kiyaye muhalli dake faruwa a yanzu." Tafkin Victoria da ke gabashin Afirka da tafkin Poyang na Sin suna fuskantar matsalolin muhalli kusan iri daya, wato kwan-gaba-kwan-bayan matsayin ruwa, da asarar mabambantan halittu da karuwar ayyukan dan Adam dake illata muhalli. Masanan Sin da Afirka suna musayar ra’ayoyi a bangarori daban-daban don magance wadannan matsaloli tare, ciki har da kyautata koguna daga dukkan fannoni da gudanar da aikin noma mai kiyaye muhalli da kayyade amfani da maganin kashe kwari da kuma amfani da makamashi mai tsabta kamar hasken rana. A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, kamfanin kasar Sin ya cimma gaggarumar nasara a bangaren samar da wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta, injunan janareto masu samar da wutar lantarki da aka harhada a tashar samar da wutar lantarki ta Busanga na kasar sun kai karfin megawatt 240, kuma suna iya samar da wutar lantarki da yawanta ya kai KWH biliyan 1.32 mai amfani da makamashi mai tsabta a ko wace shekara, matakin da ya iya yin tsimin kwal tan dubu 447, tare da rage fitar da iskar "carbon dioxide" tan miliyan 1.1 a ko wace shekara. Sin da Afirka suna rubuta sabon tarihi wajen samun jituwa tsakanin mutum da muhalli. Ba shakka, hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren kare muhalli na da makoma mai haske.(Marubuciya: MINA)
Read moreDetailsKwanan nan, babban dan kasuwar Amurka, kana babban darektan kamfanin kera motocin...
Read moreDetails'Ya'yan itacen Afirka irin su avocado, tufa, lemu, da lemu mai dan...
Read moreDetailsA babban taron AI na duniya na 2026, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, Sin za ta samar wa kasashe 30 tsarin fasahar gargadin abkuwar bala’u daga indalahhi da ake kira “MAZU’ a cikin shekaru biyar masu zuwa. A halin yanzu kuwa, "MAZU" ta riga ta fara aiki a kasashe 7 ciki har da Jibouti, Habasha da Pakistan, kuma ta baiwa kasashe sama da 40 a duniya hidimomi ta yanar gizo. Afirka daya ce daga cikin yankuna mafi fama da sauyin yanayi a duniya, inda yanayi mai tsanani ke ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar. Ma'aikacin tashar jiragen ruwa na Jibouti Mohamed Ali ya sha fuskantar rashin tabbas a kowace rana, wato zafi mai tsanani, iska mai karfi da ba zato ba tsammani, ruwan sama kamar da bakin kwarya na lokaci-lokaci da lalacewar kayan aiki da raunin jiki sun zama ruwan dare. Damina a Habasha tana haifar da ambaliya da zaftarewar kasa, wadda ke haddasa asarar rayuka da kuma gudun hijira. Shugaban hukumar kula da yanayi ta Kamaru ya bayyana cewa, "Yawancin kasashen Afirka ba su da isassun tashoshin sa-ido kan yanayi, kuma suna da karancin karfin lissafi na yanar gizo. Sai dai tsarin "MAZU" ta cika wannan gibin. A shekara ta 2025, Sin ta bai wa Jibouti kyautar tsarin fasahar "MAZU" samfurin 1.0. Tawagar kwararrun Sin ta yi bincike a wurin, tare da tsara tsarin gargadi na musamman ga tashar jiragen ruwa a wurin. Yanzu, ana iya ba da gargadin yanayi mai tsanani sa'o'i 24 kafin lokaci. Shugaban hukumar kula da yanayi ta Jibouti mai suna Nour ya ce: "'MAZU' tana da amfani sosai, kuma bangaren Sin ya horar da ma'aikata da dama ’ya’yan kasarmu." A watan Yulin bana, an mika "MAZU" Jibouti samfurin 2.0 a hukumance ga kasashen Afirka, inda aka inganta aikin hasashen yanayi, tsarin kuma yana dauke da fasahar AI, wadda ke iya tantance yanayi da kanta, da kuma ba da gargadi da kanta. Ta haka, an samar da dabarar daidaita matsala mai amfani, bisa tsarin "Bincike - sanarwa - gargadi". Sunan "MAZU" yana da ma'ana mai zurfi, MAZU a Turanci na wakiltar kalmomi 4, wato nau'ikan bala'i da yawa, gargadi, kawar da bambanci da kuma fa'ida ga kowa. Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba wannan tsari da cewa, "Dandamali, tauraron dan adam da samfuran AI na Sin sun taimaka wa kasashe da dama wajen karfafa tsarin gargadi. Wannan ita ce hanyar hadin gwiwa da duniya ke bukata, wato taimaka wa kasashe su kare al'ummarsu ta hanyar samar da fasaha da gina karfin daidaita matsala na kansu." Ba wai kawai a fannin hasashen yanayi ba, fasahar AI ta Sin tana kara shiga cikin harkokin rayuwar al'ummar Afirka. Noma a matsayin sana’ar da ke daukar kashi 45-60% na guraben aikin yi a Afirka, kuma mai ba da gudunmawar kashi 15-20% na GDPn kasashen, tana matukar bukatar AI don yin hasashen matsalar kwari da cututtuka da kuma yawan amfanin gona da za a iya girba. Saboda haka matakan da Sin ta dauka suna biyan wadannan bukatun kai tsaye. "Sin tana nacewa ga manufar sanya muradun jama’a a gaban kome da kuma kokarin cika alkawarin rage gibin AI a duniya, matakin ya yi daidai da burin ci gaban AU," in ji farfesa Gaspard Banyankimbona na kwamitin ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na kungiyar kasashen Afirka ta AU, wanda ya yaba da rawar da Sin ke takawa wajen ba da jagora a bangaren AI a duniya. Daga ma'aikacin tashar jiragen ruwa na Jibouti da ya daina damuwa kan abkuwar bala’un yanayi kwatsam, zuwa samun karfin yin gargadi da kai a yankuna masu tsauni dake Habasha, har zuwa kokarin hadin gwiwar AI na Sin da Afirka, dukkan matakan suna rage gibin dijital da amfanar da al'umma. Wannan shi ne abin da ya fi jan hankali game da hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka, wato fasahar AI ta Sin tana amfanar da al'ummar Afirka a rayuwarsu ta yau da kullum.(Marubuciya: MINA)
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.