Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ƙaramar Sallah, tare da yin kiran a ƙara ƙaimi wajen addu’o’in samun zaman lafiya a Zamfara da Nijeriya baki ɗaya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce watan Ramadan ya ba da damar yin addu’ar neman taimakon Allah kan matsalar tsaron ƙasar nan.
- Sallah: Ganduje Ya Bukaci Musulmai Su Yi Wa Nijeriya Addu’a
- Sallah: Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Fursunoni 222 Afuwa
Sanarwar ta ƙara da cewa, ya kamata al’ummar Musulmi su ci gaba da nuna kyawawan ɗabi’u da halayyen ƙwarai har bayan watan Ramadan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bikin ƙaramar sallah wani lokaci ne na farin ciki, domin yana nuna nasarar kammala azumi da kuma kusanci da Ubangiji da aka samu a cikin watan Ramadan mai alfarma.
“A ranar Idi, Musulmi suna nuna godiya ga lafiya da damar da ya ba su na sauke nauyin da aka ɗora musu na azumi.
“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin biki don inganta zaman lafiya da nuna soyayya ga juna.
“Don magance matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta, dole ne mu sa ido ga juna, mu tsaya tsayin-daka kan addu’o’inmu, sannan mu mara wa ƙoƙarin gwamnati baya na kawo ƙarshen duk wasu masu aikata miyagun laifuka.
“Ina taya ɗaukacin al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya da ma duniya baki ɗaya murna. Da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya kuma cikin ƙoshin lafiya,” in ji sanarwar.