Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta Ƙasa (NANS) ta sanar da shirin rufe dukkan manyan biranen Nijeriya daga ranar 15 ga Satumba, 2024.
A cewar NANS, wannan zanga-zangar, martani ne ga karin farashin man fetur da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya yi a baya-bayan nan.
- Kwalara Ta Yi Ajalin Mutane 7 A Jigawa
- Za A Nuna Shirin Talabijin Na Gaskiya Mai Taken “Ciyawar Kasar Sin” A Tashar CCTV-4
A ranar Talata ne dai aka samu karin farashin man fetur daga kimanin ₦568 kan kowace lita zuwa ₦855 kan kowace lita, kuma an ga wannan sauyin a duk gidajen mai na NNPC.
Wannan sauyin farashin ya haifar da cece-ku-ce a duk fadin Nijeriya inda ƙungiyoyin kwadago suka ce hakan sam ba za ta sabu ba, dole a sauya sabon farashin nan take.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Okunomo Henry Adewumi, shugaban majalisar NANS, ya bukaci a gaggauta janye sabon farashin man fetur din nan take.
Sanarwar ta ce, za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana da bin doka kan wannan sabon farashin man fetur din idan har ba a janye sabon farashin ba.