Shugaban kungiyar kwadago, NLC reshen jihar Kebbi, Kwamared Murtala Usman, ya ce, karin kudin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya ta yi, zai zama sakamakon illata tattalin arzikin Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin kungiyoyin NLC da kungiyar ‘yan kasuwa, TUC da sauransu suka hana shiga da fita a ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KAEDCO) da hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya NERC a Birnin Kebbi.
- Sin Da Amurka Za Su Gudanar Da Tattaunawa Ta Farko Ta Manyan Jami’an Gwamnati Dangane Da Fasahar AI
- ‘Yansanda Sun Tsare Habashawa 24 A Dajin Kenya
“Ƙarin kuɗin wutar lantarki yana haifar da sauyin farashin komai a Nijeriya, tun daga ƙarin farashin kayayyaki, farashin sufuri da sauran su yayin da yawancin ‘yan Nijeriya za su shiga cikin duhu saboda rashin iya biyan kuɗin da aka kara.” In ji Kwamared Murtala
Kwamared Usman ya tunatar da gwamnati cewa, kudin al’umma ne ake samar da man fetur da wutar lantarki, kuma dole ne ‘yan kasa su samu sauki da kuma walwala a cikin tattalin arzikin kasarsu. Ba wai ‘yan kasa su rika shan wahala ba.