Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 domin ta magance buƙatun ta.
ASUU ta ce matakin ya biyo bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da ta gudanar a ranar Lahadi a jami’ar Abuja.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma rabawa manema labarai a ranar Litinin.
Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in.
Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp