• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato

by Shehu Yahaya
4 months ago
Lauyoyi

Kungiyar Lauyoyin Musulmi ta Kasa (MULAN) reshen Jihar Kaduna, ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa matafiya a Jihar Filato, inda ta bayyana harin a matsayin rashin tausayi da imani.

Kungiyar ta yi Allah wadai ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar, Barista Awwal Tesleem Shittu ya raba wa manema labarai a Kaduna. 

  • Gwamnan Kaduna Ya Yunkura Don Warware Matsalolin Rashin Aikin Yi Ga Matasa – Dan Isan
  • Majalisa Ta Yi Allah-wadai Da Kashe Wasu Matafiya ‘Yan Kaduna 13 A Jihar Filato

A cewar sanarwar, harin ya faru ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuni, 2025, lokacin da wata motar bas mai kujeru 18 dauke da fasinjoji daga Basawa na Jihar Kaduna.

“Muna tunawa, da bakin ciki, irin wannan ta’asa da aka yi a baya, inda aka yi wa matafiya da ba su ji ba gani ba, kwanton bauna ba tare da an hukunta su ba.”

Sanarwar ta kara da cewa sake faruwar hare-haren da aka tsara da kuma niyya, musamman a Jihar Filato, alama ce mai hatsarin gaske da ke nuna cewa masu aikata laifuka da ‘yan ta’adda suna sake kwarin gwiwa sakamakon gazawar gwamnati na ci gaba da aiwatar da rashin bin doka da oda

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

“Muna bayar da wannan a matsayin gargadi kai tsaye ga gwamnatin Nijeriya a matakin tarayya da na jihohi. Ka da a bari a zubar da jinin wadannan ‘yan Nijeriya marasa laifi ya tafi a banza.”

Shittu, ya lura da cewa hakurin al’ummomin da ake ci gaba da yi wa kisan gilla ba shi da iyaka, ya kara da cewa rashin kamawa da gurfanar da masu aikata laifukan tare da hukuntansu yana nuna gazawar gwamnati.

“Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, kuma na gaskiya kan wannan kisan kiyashi da kamawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da alhakin wannan danyen aikin.

 “Muna san a biya isasshiyar diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, haka kuma a tura jami’an tsaro na dindindin a duk wuraren da ake kisa a Filato da jihohin makwabta.

“Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara zage damtse na ganin ta magance yawaitar kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan baki daya” in ji sanarwar. 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.