Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da suke aiki a su.
A sakamakon haka, an kulle ƙofar shiga shalƙwatar hukumar NUPRC da ke Abuja, inda ɗaruruwan ma’aikata suka taru a waje ba tare da an bari sun shiga ba. Wannan mataki ya haddasa tsaiko a gudanar da ayyuka, musamman a sashen kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasar.
- Rikicin Dangote Da PENGASSAN Ba Zai Kawo Wahalar Fetur Ba
- Majalisa Ta Daƙile PENGASSAN Akan Shirin Daina Kai Wa Matatar Ɗangote Gas Da Ɗanyen Mai
PENGASSAN ta bayyana cewa yajin aikin ya samo asali ne daga korar kusan ma’aikata 800 a Matatar Man Dangote, inda aka zargi kamfanin da maye gurbinsu da baƙi daga ƙasashen waje. Ƙungiyar ta ce wannan lamarin babban cin zarafi ne ga dokokin ƙwadago na Nijeriya da na Ƙungiyar Kwadago ta Duniya (ILO).
Sakatare Janar na PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, ya yi kakkausar suka ga Matatar Dangote, yana mai zargin kamfanin da korar ma’aikatan ne saboda shiga ƙungiyar ƙwadago. Ya ce wannan doka ce aka karya, tare da tabbatar da cewa ƙungiyar ba za ta janye daga yajin aikin ba sai an warware matsalar tare da dawo da ƴan uwansu bakin aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp