Wasu ‘Ƴan bindiga sun kai hari unguwar sabon garin Kano sun harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a Jihar Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:45 na dare a daidai rukunin ginin kantina na Azubros da ke Titin France a Sabon Garin Kano.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 60, Sun Kashe 4 A Neja Da Kaduna, Sun Bukaci Kudin Fansa Miliyan 200
- ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Hadimin Gwamnan Bauchi, Sun Jikkata Mutum 1
Shaidun gani da ido sun ce ‘ƴan bindigar sun iso wajen ne, sannan su ka harbe shi, inda ya mutu nan-take, su kuma su ka tsere.
“Dama, kana gani ka san shi su ka zo kashewa. Shahararren mai sayar da batira ne a Sabongari ,” inji shaidun gani da ido.
Jaridar bata samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘ƴan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa ba a lokacin haɗa rahoton.