Ɗalibai ‘yan asalin ƙananan hukumomin Musawa da Matazu masu karatu a manyan makarantun gaba da sakandare zasu amfana da tallafi daga gidauniyar ɗan majalisar tarayya Hon. Abdullahi Aliyu (Talban Musawa).
Wannan tallafi dai kimanin ɗalibai 1,991 da suka fito da mazaɓu 21 da ake da su a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu kuma waɗanda suke Karatu a manyan makarantun gaba da sakandare ne za su amfana da shi.
- Zargin Daura Aure Da Mai Kanjamau: Yadda Aka Tube Hakimi A Katsina
- Wa Ya Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina?
Shugaban kwamitin ilimi na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan hukumomin Musawa, dakta Samaila Adamu Dangani, ya bayyana cewa wannan wani tallafi ne na gidauniya ɗan majalisar domin tallafawa iyaye da ɗalibai.
Ya ƙara da cewa kimanin ɗalibai 1,087 ne suka fito daga ƙaramar hukumar Musawa a ya yin da 808 suka fito daga ƙaramar hukumar Matazu kuma dukkan su an tantance su, kuma sun tsallake ƙa’idojin da aka shinfiɗa don cin gajiyar tallafin.
A cewarsa masu karatun digiri da babar difloma (HND) zasu samu tallafin naira dubu ashirin (20,000) sai kuma masu karatun NCE da ƙaramar difloma (ND) kowanensu zai samu tallafin dubu sha biyar (15,000).
“Ina son na yi amfani da wannan damar na sanar da al’umma cewa tun farko, mun samu adadin ɗalibai 2,364 amma da aka yi aikin tantancewa shi ne mutum 1,991 suka samu nasara kuma sune za su amfana da wannan tallafi” inji Ɗangani
Dakta Samaila Adamu Dangani ya yi ƙarin haske da cewa wannan tallafi bai nuna bambanci siyasa ba, in dai mutum ya cancanta ko daga wace jam’iyya yake zai amfana matsawar dai ɗan asalin ƙananan hukumomin Musawa da Matazu ne.