Wani mummunan lamari ya afku a Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD), da ke Jihar Jigawa, inda wata daliba ta haihu a dakin kwanan ɗalibai sannan ta jefo jaririn daga saman wani bene mai hawa uku wanda ya yi sanadiyar mutuwar jaririn.
A jiya Litinin, wani faifan bidiyo ya yaɗu da ke nuna wannan mummunan al’amari, inda ɗalibai mata suka taru kusa da gawar jaririn, suna kokarin fahimtar wannan mummunan lamarin.
- Boko Haram Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Maiduguri Zuwa Kano
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Abuja Zuwa Nasarawa
Ɗalibar, wacce aka boye sunanta, ta haihu ne a dakin kwanan ɗalibai mata, kuma bayanai sun nuna cewa dalibar ba ta yi aure ba, lamarin da ya bar baya da ƙura na tambayoyi game da yanayin cikinta da kuma haihuwar.
Kakakin Jami’ar Tarayya Dutse, Abdullahi Yahaya Bello, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana cewa hukumomin jami’ar sun sanar da ‘yansanda, tare da jaddada cewa ɗalibar ba ta dauki ciki a jami’ar ba, inda ya ce watanninsu biyu kacal da komawa zangon karatu.
Ya ƙara da cewa, bayan faruwar lamarin, nan take aka kai ɗalibar asibiti domin duba lafiyarta, inda jami’ar ke ci gaba da bincike don ɗaukar matakan da suka dace na shawo kan lamarin.