Dan majalisar Tarayya da ke wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal a majalisar wakilai, Honarabul Abdussamad Dasuki ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke ci-gaba da kisan al’umma ba ƙaƙƙautawa a Sakkwato.
Dasuki ya bayyana haka ne a ranar Litinin a yayin da yake jajantawa al’ummar mazaɓarsa a gundumar Kuchi da Jabo wadanda hare- haren ‘yan ta’adda ya shafa a kwanan nan.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
- Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin
Honarabul Dasuki wanda ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa a sansanin ‘yan gudun hijira a Kuchi da ke Karamar Hukumar Kebbe da Jabo a Karamar Hukumar Tambuwal ya ba su tallafin agajin gaggawa na kayan abinci domin rage masu radadi.
Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.
Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.
“Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen wannan ta’addancin.”
Dan Majalisar ya ce ya gabatar da bukata ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa domin tallafawa wadanda lamarin ya shafa kuma zai ci- gaba da bibiya domin ganin tallafin ya samu cikin lokaci.
Ya ce yana kokarin ganin rundunar sojoji ta kara tura wadatattun jami’ai tare da tallafa masu domin yakar ‘yan ta’addan da wanzar da zaman lafiya a yankunan.
Tallafin kayan abinci na gaggawa da dan majalisar ya bayar sun hada da buhuhuwan masara, gero, garin kwaki da kuma kuli- kuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp