A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sabon zababben kantoman yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin John Lee a nan birnin Beijing.
John Lee, ya zamo kantoman yankin musamman na Hong Kong na 6, bayan lashe zaben ranar 8 ga watan nan na Mayu, zai kuma kama aiki a ranar 1 ga watan Yulin shekarar nan. Â (Saminu)