Lamarin kalle-kalle da karance-karancen batsa ya wuce gona da iri a cikin al’umma, abin ban haushi da ban takaici a cikin masu ta’ammali da kafofin na sadarwa an rasa tsayayyun masu fada a ji da za su fito su ci gaba da wayar da kan mutane a kan wannan iftila’in da yake neman kassara al’ummarmu, kai wallahi zan iya cewa ma ya kassara mu.
Wallahi abin yana kuntata mani, ba karamar damuwa nake shiga saboda lamarin ba, wallahi wani abun ba ma zai fadu bane, wanda ba ka tunani shi za ka gani da BF a cikin wayarsa, ko kuma in wayarsa ta shiga hannunka a bisa hadari kuma aka yi gam da katar ka shiga Browser din wayarsa sai ka yi da na sanin shigar wayar hannunka, uwa uba idan ka shiga history na wuraren da ya shiga na browsing, za ka abin takaici da ban haushi, kuma ba mazan ba ba matan ba, ba manyan ba ba yara ba, ba gwagware ba ba ma’aurata ba, kuma kar ma ka min comment cewa baka yi, ban bukaci in ji hakan ba, kawai ka saurari nasihata.
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
- 2023: Za A Fara Shirye-shiryen Aikin Hajji Ranar 21 Ga Disamba – NAHCON
Su dai wadannan abubuwan da muke ta kalla na banza, wallahi har yanzu kun kasa gano cewa da BF da American Film duka masana’anta ce take samar da su domin yin business, yadda za a biya actor a film din Action haka za a biya actor na Film din BF, yadda actor na film din India zai je ya biya kudi ya sayi kayan karfe domin ya hada kwanji yadda za a bashi acting a film na fada haka actor na BF zai je asibiti ya biya kudi a kara masa karfin mazakuta dinsa saboda da ita yake neman abinci, haka yadda mace take kiyaye jikinta a industry na Bollywood ta hanyar motsa jiki da cin abinci mai gina jiki da sauran abubuwa domin ta kiyaye kyanta da lafiyar jikinta ta yadda za ta samu karbuwa a wajen directors haka actress din BF take zuwa asibiti ta biya kudi a yi mata tiyata a gyara mata mamanta a kuma bata kwayoyin sha domin hana maman nata zubewa, haka zalika duk wani pribate part nata tana biyan makudan kudade ne a yi mata gyara na musamman da zai janyo hankalin directors na wannan masana’antar su kara bata role da zata yi.
Yadda ka san Aminu Saira zai zauna ya yi tunani ya tsara labarin film a Kannywood, haka wani kato zai ci ya koshi sai ya tsara labarin film din BF, sai a nemo actors da actresses su zo su buga roll, kowanne a sallame shi ya kara gaba.
Sabanin yadda kuke tunani, BF ba lokaci daya ake tsara shi ba, kamar yadda ake shooting din Kannywood film haka ake shooting BF, in an yi fita ta daya, actor ya yi kuskure a cikin roll da director ya bashi ko actress sai an sake, kuma edactly yadda suke yi a farko haka za su sake maimaitawa.
Bari na baku misali yadda za ku fi fahimta, Idan aka ba actor cewa kalar kwanciya kaza ake so ya yi da matar kuma waje kaza da kaza zai taba, to idan ya kuskure bai yi daya daga cikin abinda aka bashi a script ba to sai an sake dauka, ko kuma misali ace idan ya tara da ita a daidai lokacin da zai yi inzali ana so ya fitar da gabansa daga gabanta ya yi inzali a waje, idan ya kasa control din kansa ya kasa cirewa a daidai lokacin to sai an sake sabon dauka.
Haka mace, idan aka ce ana so misali ta yi kwanciya kaza ko ta yi kalan wasa kaza da namijin a lokacin da yake inzali, idan bata iya yi ba maybe ita ma a lokacin take releasing sai an sake sabon lale!
Wannan yake tabbatar mana da cewa suma ba wai dadin abinda suke yi suke ji ba, kawai neman kudi suke yi da hakan, mu kuma dolaye sai kalla muke yi muna jin dadi ana ihun banza wai a tunaninmu dadi suke ji!
Na’am bana kore bukatuwar namiji ga mace da kuma bukatuwar mace zuwa ga namiji, domin wannan halitta ce da Allah ya halicce mu da ita, dan haka wannan mu’amalar babu makawa sai an yita, to amma abin damuwar shi ne, yay a kamata a yi, kuma mene ne gaskiya mene ne kuma karya a abinda ake nuna mana a wannan fina-finan?
Da farko tabbas duk halittar da za ka iya gani ga masu wannan sana’ar to da tasirin surgery ko wani special treatment da aka yi musu a wannan halittar, kuma kai ma idan kana so za ka iya mayar da mazakutarka kamar tasu idan za ka iya biyan wannan makudan kudaden da suke biya, haka kema idan kina bukatar mamanki da sauran pribate parts dinki su zama irin nata to za ki iya biya a yi maki, amma fa ku san wani abu, komin daren dadewa sai wannan aikin ya dawo baya zuwa ga asalinku, sai dai idan za ku ci gaba da kashe wannan kudin ne har karshen rayuwarku to ga fili ga mai doki.
Amma babbar matsala wannan treatment da shan magunguna din ita ce; da farko dai idan ka sha magani da sunan neman karfin mazakuta wai dank a ga wani actor a BF yana da girman mazakuta, ba lallai matarka ta biya maka bukatarka ba, domin ba z aka gamsu da juriyarta ba, ita kuma in ka matsa mata za ka cutar da lafiyarta, daga nan sai neman mata, idan kuma mace c eke to mijinki ba zai taba gamsar da ke ba, daga nan sai neman maza {Allah ya kare mu}.
Ta bangaren marasa aure kuma shi ne, ba lallai ne matar da z aka aura ta kasance za ta gamsar da kai ba, haka kema ba lallai mijin ya gamsar da ke ba, kuma wannan ba karamin tasiri yake ba wajen nesantar juna matukar ba a samun biyan bukatar juna a kwanciya, a haka sai abu ya girma a kai ga rabuwa.
Sannan idan ya zamana namiji ya saba da wannan kallon, wallahi idan ba kalla yay i b aba zai samu kwanciyar hankali a bangaren sha’awa ba koda kuwa yana da mata, zai zama matar bata da rana haka zai kyale ta cikin damuwar rashin biya mata bukatarta, haka ita ma idan ta saba wallahi mijin ba zai gane komai ba, kuma ba zata samu biyan bukata ba in dai ba ta wannan hanyar ba.
Abinda ya sanya ba zan tabo maganar masturbating ba ko kuma istimna’i saboda abu biyu ne a jere, duk wanda yake kallon BF to tabbas yana istimna’i, koda ya kasance ba kowanne ba mai masturbating ne yake wannan kale kallen ba, haka abinda ya sanya ban kawo bangaren karanta rubuce-rubucen batsa ba da ake karantawa saboda dukansu aiki daya suke yi a tunanin mutane na biyan bukata ko kasha sha’awa wai.
Aiki ne mai girma a kanmu, mu guji wadannan abubuwan ko dan lafiyarmu, haka zalika mu yi kokarin hana na tare da mu kusantar wadannan abubuwan ta hanyar tsoron Allah, aure ko azumi, domin wadannan ne kadai katangar kare kai daga fadawa wannan halakar, Allah ya tsare mu.
To abin tamyar a nan shi ne; Ina matsalar take?
Za ka ga namiji iya namiji, kamili da tsoron Allah da kyautata wa iyaye da makwabta, ga taka tsan-tsan da lamurran duniya, amma kuma sai tsautsayi ya hada ka da wayarsa ka sha mamaki, haka zalika za ka ga mace kamila cikin hijabi maybe ma har da nikabi, ga shiga ta kamala iya shiga amma idan gam da katar ya sa ta zo wajanka da wayarta domin ka gyara mata wani abu kuma aka hadu da la haula sai ka ga abinda zai gigita ka!
Abin ban takaici za ka ga yaro wanda bai wuce shekara 14 ba amma idan ka duba wayarsa za ka yi mamaki musamman idan ka shiga history na bisited sites, kuma abin ya zama ruwan dare, wai me ye matsalar ne?
Da farko babu babban abinda yake kawo abin ga yara kanana face dayan abu uku:
1- Iyayen suna yin mu’amala a gaban yaro irin ta ma’aurata tun yana karami har ya fara fahimtar abubuwa kuma basu sanya kula wajen hana shi ganin abin ba, domin yin hakan yana matukar girmar da sha’awar yaro kafin lokacinta ya yi, iyaye mu kula da wannan sosai, yaro a lokacin da ya kai shekara biyu kwakwalwarsa tana matukar haddace abubuwa, kuma abin yana rika dawo masa, sai shima ya yi kokarin gwada abinda ya ga kuna yi.
2- Ko kuma yaron iyaye ba sa bashi kulawa irin wacce ta dace da har zai kasance karkashin matakan tsaronsu, tare da rashin tsananta bincike a kan lamarin yaron.
3- Ko kuma ya kasance yaron ya hadu ne da miyagun abokanai, sai su canza masa tunani tare da lalata rayuwarsa ba tare da sanin iyayen ba.
Matakin dauka a nan a bayyane yake, iyaye su lura da mu’amalar da za su rika yi da junansu a gaban dadansu, sannan su sanya tsaro na musamman ga yaransu, tare da lura da shige da ficen yaron, abokansa, da wa yake mu’amala, kuma me yake aikatawa a ciki da wajen gida.
Ta bangaren manya da basu da aure, mafi yawan abubuwan da suka fi janyo wannan dabi’ar su ne:
1- Tunanin cewa hakan zai rage musu sha’awar da ke tare da su, a karamin hangensu shi wannan aikin wai kamar zai taimaka musu wajen danne sha’awarsu.
2- Tunanin cewa hakan zai hana su aikata zina, sai suke amfani da wannan wai a tunaninsu dan magance wannan damuwar da hana kansu afkawa wannan aika-aikar.
3- Tunanin cewa wannan aikin kamar yana samar da lafiya ta hanyar fitar da mataccen maniyyin da mutum ya tara.
4- Shagala irin ta zuciya, tare da jahiltar me ye wannan abin.
5- Rashin sanin illoli da cutarwar wannan aikin.
Da ma wasu dallilai da ban ambata ba, amma dai kusan wadannan da na ambata gaskiya su ne wadanda matasanmu suka fi fama da su.
Ta ya mutum zai iya guje wa wannan matsalar?
Da farko dai sai da addu’a, domin fin karfin zuciya abu ne da babu abinda ya fi shi wahala, idan ba da taimakon Allah ba wallahi mutum ba zai iya ba, sannan kuma sai kyakkyawar niyya da aniyar denawa din, domin duk yadda mutum yake son yin abu idan bai yi azama kuma ya dake ba to ba zai iya ba, kazalika mutum ya guji duk wata hanya da zata kai idonsa ko kunnensa zuwa ga abinda zai iya haifar masa da komawa zuwa ga wannan aikin, ta hanyar guje wa shafukan da suke dauke da wannan kalar content din, goge duk wani abu da zai iya bijiro da tallar irin wadannan abubuwan ko kuma takaita shafukan a hankali a hankali har mutum ya guje su baki daya.
Sannan abu mai muhimmanci, duk wanda wannan dabi’ar ta kama to lallai wallahi yana da bukatar yin aure cikin gaggawa, domin hakan ne hanya mafi sauki kuma mafi sauri wajen fita daga wannan ashha din.
Haka zalika lizimtar azumi yana da matukar tasiri, mutum ya tsara wa kansa tsari mai kyau domin yaki da wannan mummunar dabi’ar.
Idan kuma duk wannan bai yi amfani ba, to mutum ya je na nemi likita ya bashi magungunan taimako domin rage sha’awar, duk da cewa suna cutarwa suma, amma cutarwarsu bata kai ta cutarwar wannan dabi’ar mai haifar da cutarwa ga pribate part ba, cutarwa kuma mai matukar wuyar warkewa.
Sannan kuma mutum ya nemi magani, domin wanda yake kale kallen banza tabbas yana aikata istimna’i {masturbating}, kuma mai aikata wanan lallai yana daukar cututtuka da daman gaske, mafi karancinsu shi ne rashin haihuwa da kuma lalacewar al’aura!
Su kuma masu aure, a iya abinda na sani manyan dalilan yin wannan dabi’ar a wajensu su ne:
1- Kasancewar tun asali tun kafin aure an saba da wannan dabi’ar har ta zamo jiki ta yadda ba za a iya rabuwa da ita ba, hakan yana sa abin ya zama jiki ga mutum, ya kasance kwata-kwata ba a jin dadin juna a kwanciyar aure, mai wannan dabi’ar duk yadda abokin rayuwarsa zai yi kokari wajen sauke nauyinsa a wannan janibin to shi fa ba zai samu kwanciyar hankali ba sai ya yi wannan dabi’a din.
2- Rashin samun gamsuwa daga wajen abokin rayuwa a kwanciyar aure, wanda hakan yana iya jefa abokin rayuwar cikin halin kunci da damuwa ta yadda zai kasa jurewa a yanayin da yake rayuwarsa, dan haka sai ya fara aikata hakan koda dama can ba dabi’arsa ba ce, duk da wannan mawuyacin abu ne ka samu irin haka gaskiya.
3- Karancin tsoron Allah da son zuciya, wanda za ka ga mutum abokin rayuwarsa yana yi masa komai na rayuwa amma duk da haka yake iya yin karfin halin aikata wannan abin, ba dan komai ba sai dan biyewa son zuciya.
4- Auren dole yana matukar taka rawa wajen kawo wannan matsalar musamman ga ‘ya mace, kuma musamman ma ace tana ta’ammuli da shafukan sadarwa, kuma tana da ra’ayin irin kalle-kallen nan ko karance-karancen banza.
Domin magance wannan, a dage da addu’a da kuma kyakkywar niyya da guje wa abin, haka kuma a nemi magani, domin mai aure tasirin cutarwar wannan abin yana bayyana a garesa nan take fiye da marar aure, sannan a kula da inda ake shiga a shafukan yanar gizo, a tsaurara matakai wajen kiyaye kai daga hango abinda zai iya kawo tunanin aikata wannan abin, sannan duk lokacin da mutum ya ji cewa yana son yin wannan aikin to ya yi kokarin tashi daga wajen da yake ya dan fita waje ya motsa jininsa, hakan yana taimakawa wajen dakusar da wannan abin.
Allah ya taimake mu ya sa mu fi karfin zuciyarmu.