An kona ofishin yakin neman zaben Mohammed Barde dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Gombe.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bangar siyasa, sun kona ofishin da ke kusa da masaukin shugaban kasa na gidan gwamnatin Gombe a safiyar ranar Litinin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto akwai zarge-zarge da dama kan harin, amma jam’iyyar PDP ta dora alhakinsa kan jam’iyyar APC mai mulki. Daily Trust ta rahoto
A wata sanarwa da Barde ya fitar, ya tabbatar da harin, inda ya ce an lalata kayan dukiyoyi da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp