• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Ibo Mazauna Kano Sun Goyi Bayan Takarar Atiku

by Sulaiman
3 years ago
Atiku

Al’ummar Ibo mazauna Jihar Kano sun bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a babban zaɓen da za a yi a wannan watan.

 

Sarkin Ibo na Kano, wato Eze Ikechukwu Akpudo, shi ne ya bayyana haka a madadin al’ummar tasa a lokacin da sarkin yaƙin rundunar zaɓen Atiku a Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali-Amin (Little), ya kai masa ziyara a fadar sa.

  • Akwai  Wasu Kusoshi A Fadar Shugaban Kasa Da Ke Goyon Bayan Atiku – Wike

Eze ɗin ya bayyana Atiku da cewa wani kadarko ne wanda ya yi aiki matuƙa wajen kawo haɗin kai a ƙasar nan.

 

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

Ya ce: “’Yan Nijeriya ba su da zaɓin da ya wuce Atiku, domin shi kaɗai ne wanda zai iya doke Tinubu a zaɓe. Ya na takara a babbar jam’iyya.

 

“Wani dalilin kuma shi ne ba za mu iya goyon bayan tsarin takarar Muslim-Muslim ba. Mu na so a samu takara mai daidaito domin tabbatar da adalci ga kowa da kowa.

 

“Kamar yadda ku ke gani, kwanaki kaɗan ne su ka rage kafin a yi zaɓe, amma babu wani daga cikin mu da zai tashi ya koma garin su domin yin zaɓen. A nan za mu yi zaɓen tare da iyalan mu. Nan za mu tsaya, a nan mu ke harkokin kasuwancin mu.

 

“Addu’ar mu ita ce a yi zaɓe cikin lumana. Mun yanke shawarar cewa Atiku Abubakar kaɗai ne zai iya tunkarar matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a yau.

 

“Mu na magana ne da murya ɗaya a matsayin mu na al’umma ɗaya. Ba mu yin wata ƙunbiya-ƙunbiya a magana, kuma mu na ba mai girma Atiku tabbacin cewa shi za mu ba ƙuri’un mu.

 

“Ni ɗin nan sau biyu ana zaɓa ta a matsayin kansila a Sabon Gari. Zan tattaro jama’a bakin iyawa ta don ganin Atiku ya samu nasarar lashe zaɓen da za a yi.”

 

A nasa ɓangaren, Ali-Amin Little ya bayyana cewa ‘yan ƙabilar Ibo mutane ne masu son zaman lafiya kuma sun yi fice a harkar kasuwanci.

 

Ya yi kira a gare su da su yi amfani da ƙuri’ar su yadda ya kamata domin su samu cin moriyar mulkin dimokiraɗiyya tare da sauran al’umma.

 

Ya ce: “Atiku Abubakar zai yi tafiya tare da dukkan ƙabilu idan ya zama shugaban ƙasa. Ƙasar nan ta yi masa komai na rufin asiri, don haka shi ma ya ke so ya mayar mata da sakayyar alheri ta hanyar samar da shugabanci mai nagarta da alfanu ga ‘yan Nijeriya.

 

“Hakan ne ya sa ya ke auren mace Ibo, da Bayarabiya da Kanuri, da sauran su. Shi Waziri mutum ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su amince da shi saboda amfanuwar ƙasar da haɗin kan ta.”

 

Wasu waɗanda su ka take wa Al-Amin Little sawu a lokacin ziyarar sun haɗa da Dakta Auwalu Anwar, wanda shi ne mai ba Atiku shawara a ɓangaren tsare-tsare, da kuma Alhaji Bashir Kalla.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
Siyasa

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Next Post
Kwalliyar Doguwar Rigar Abaya

Kwalliyar Doguwar Rigar Abaya

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.