Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da sanarwar cewa za ta damƙa wa zaɓaɓɓun-gwamnoni satifiket ɗin shaidar lashe zaɓe a ranakun Laraba, 29 ga Maris, Alhamis 30 ga Maris da kuma Juma’a, 31 ga Maris.
Sanarwar ta ce kuma duk a waɗannan ranaku ne za ta bayar da satifiket ɗin ga mataimakan zaɓaɓɓun-gwamnoni da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Babban Jami’in Wayar da Kan Jama’a kuma Jami’in Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Asabar.
Ya ce Hukumar Zaɓe za ta raba masu katin shaidar lashe zaɓen ne bisa ƙa’idar da Sashe na 72(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.
Sashen dai ya ce, “tilas INEC ta damƙa masu satifiket na shaidar nasarar lashe zaɓe cikin kwanaki 14 bayan nasarar da su ka samu.”
Okoye ya ce INEC za ta raba masu satifiket ɗin a ofishin INEC da ke jihohin su.
Ya ce Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su za su sanar da su ranar da za a bai wa kowanen su.
An dai yi zaɓen a ranar 18 Ga Maris, inda zuwa yanzu jihohin Kebbi da Adamawa ne kaɗai ba a bayyana sakamakon zaɓen gwamna ba, saboda sai an yi ‘inkwankilusib’.