Yayin da ya rage saura wata ɗaya a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da na mambobin majalisar tarayya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara cewa su guji take dokoki, musamman dokokin da hukumar ta haramta a lokacin kamfen.
Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata hira da PUNCH a ƙarshen makon da ya gabata.
Za a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da mambonin majalisar tarayya a ranar 28 Ga Satumba, yayin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Okoye ya bayyana cewa wuraren da dokar INEC ta hana yin kamfen da tarukan siyasa sun haɗa da coci-coci, masallatai, gine-gine da ofisoshin gwamnatin tarayya, na jihohi ko ƙananan hukumomi da kuma amfani da mutum-mutumin ‘masquarade’.
Ya ce ya zama wajibi jam’iyyu da ‘yan takara su bi ƙa’idojin da Dokar INEC ta 2022, Sashe na 92 ya gindaya.
Daga cikin sharuɗɗan da Okoye ya jaddada, akwai “yin hani da amfani da mutum-mutumin domin ƙara wa taron siyasa armashi, yin amfani da wuraren ibada, ofisoshin gwamnati ko gine-ginen gwamnati domin yi wa ma’aikata kamfen da sauran su.
“Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana rubutawa ko rera taken jam’iyya ko na ɗan takara ɗauke da kalaman zagi, cin fuska ko aibata wani ɓangaren addini, yare, ƙabila ko wani yankin jama’a.
“Ba a yarda a riƙa amfani da zage-zage a lokacin kamfen ko tarukan siyasa ba. Kuma banda kalaman da ka iya harzuƙa wani ko wasu gundun jama’a su hasala har su tayar da hargitsi. A guji amfani da yare ana cin zarafin wani yare, kuma banda shaguɓe da kalaman aibatawa da ka iya harzuƙa wasu ɗaukar doka a hannun su.
“Sashe na 3 na wannan doka ya haramta kamfen ko tarukan siyasa a wuraren ibada, ofishin ‘yan sanda, ofisoshin gwamnati da gine-ginen gwamnati. Saboda haka ba a yarda a tallata jam’iyya ko ɗan takara a waɗannan wurare ba.
“Sashe na 2(5) kuma ya haramta jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da ‘yan daba ɗauke da makamai. Kada jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da wasu jami’an tsaro masu zaman kan su ɗauke da makamai a wurin kamfen, taro ko wurin zaɓe.
“Sashe na 7(a) (b) da kuma Sashe na 8 sun jaddada cewa duk wanda ya karya Sashe na 92 za a yi masa tarar naira miliyan 1 ko ɗaurin shekara 1, idan ɗan takara ne.
“Idan jam’iyya ce ta karya dokar, za a yi mata tarar naira miliyan 2. Idan ta ƙara kuma tarar naira miliyan 1.
“Wanda aka kama ya tayar da hargitsi ko ya yi amfani da makami kuma za a yi masa tarar naira 500,000 ko ɗaurin shekaru uku, ko kuma a haɗa masa duka biyun.” Inji Okoye.