Gabanin wa’adin ranar 17 ga watan Yuli da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba wa jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu na zaben 2023, kungiyar goyon bayan Tinubu ta amince da a zabi gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin mataimakin Tinubu dan takarar shugaban kasa.
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, ya fito fili ya bayyana cewa har yanzu yana neman abokin takararsa.
Majiyoyi a cikin jam’iyyar APC sun ce dan takarar jam’iyyar yana son daukar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ko kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima.
Amma da yake magana yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin a Kaduna, Darakta-Janar na kungiyar magoya bayan Tinubu (TSO), Aminu Suleiman, ya ce kungiyar ta yanke shawarar zaben El-Rufai ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewa maso yamma da sauran su.
Suleiman Ya yi imanin cewa zabar abokin takara na da matukar muhimmanci ga nasarar Tinubu a 2023, don haka kungiyar ta tantance duk wani zabin da za ta yi na son mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito daga yankin Arewa maso Yamma, shiyyar itace mafi yawan kuri’u a duk fadin Nijeriya.
Kungiyar ta kara da cewa, El-rufai gogaggen mutum ne da ya taka rawar gani a fagen siyasa da mulki a matakin tarayya da jiha kuma shi ne dan takarar da ya dace da Tinubu a matsayin mataimakin shugaban kasa.